Matashin da ya kashe matar mahaifinsa ya gurfana gaban kotu

An gurfanar da matashin nan da ake zargi da kashe matar mahaifinsa ta hanyar caccaka mata lauje a gaban Kotun Majistare ta Nomansland da ke Kano. dan sanda mai gabatar da kara Sufeta Shu’aibu Musa ya shaida wa kotun cewa wanda ake zargin Sagiru Wada Abdullahi na Unguwar Kurmawa a birnin Kano ya yi amfani […]

Matashin da ya kashe matar mahaifinsa ya gurfana gaban kotu
Matashin da ya kashe matar mahaifinsa ya gurfana gaban kotu

An gurfanar da matashin nan da ake zargi da kashe matar mahaifinsa ta hanyar caccaka mata lauje a gaban Kotun Majistare ta Nomansland da ke Kano. dan sanda mai gabatar da kara Sufeta Shu’aibu Musa ya shaida wa kotun cewa wanda ake zargin Sagiru Wada Abdullahi na Unguwar Kurmawa a birnin Kano ya yi amfani da lauje inda ya sassara wa matar mahaifinsa mai suna Zainab Wada sau biyar a kai a
lokacin da take barci lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarta. Mai gabatar da karar ya cewa bayan aikata laifin wanda ake zargin ya yi kokarin gudu inda ’yan uwansa suka kama shi suka mika ga ’yan sanda.
Lokacin da aka waiwaiyi wanda ake zargin ya musanta laifin da ake zarginsa da shi, laifin da ya saba wa sashi na 221 na Final Kod. Sufeta Shu’aibu ya nemi kotu ta sanya ranar da za a ci gaba da sauraren karar don ba shi damar fara gabatar da shaidunsa. Alkalin Kotun Mai shari’a Maryam Ahmad Sabo ta sanya ranar 8 ga Agusta don ci gaba da sauraren shari’ar tare da bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake zargi a kurkuku.