Matashin da ya sare hannun kanen mahiafinsa ya shiga hannu

Wani matashi da ya sare hannun kanen mahaifinsa da adda bisa zargin maita ya shiga hannun ’yan sandan a Jihar Katsina.

Matashin da ya sare hannun kanen mahiafinsa ya shiga hannu

Wani mutum rike da adda

Wani matashi da ya sari kanen mahaifinsa da adda a hannu bisa zargin maita ya shiga hannun ’yan sandan a garin Jangefe da ke Karamar Hukumar Batagarawa a Jihar Katsina.

Kamar yadda ya fada da bakinsa, matashin ya ce yana zargin kanen mahaifin nasa da maita, inda yake kama ’yan gidansu, ciki har da har da mahaifiyar matashin.

“Mahaifiyata ta kamu da rashin lafiya bayan shigowar shi kanen mahaifin nawa gidan ya fita, kuma ta rika ambaton sunan shi kanen mahaifin nawa.

“Da ma duk wani dan gidanmu da ya kamu da rashin lafiya sai ya rika ambaton sunansa. Wannan ne ya sa nike zargin shi da yin maita,” in ji shi.

A cewarsa, ya je gidan kanan mahaifin nasa ne inda bayan ya yi mashi sallama ya fito ya nemi su kebe domin yana son magana da shi, amma sai ya ki yarda ya bi shi inda ya so su je.

Nan take ya bayyana mishi zargin da yake masa, sannan ya kai mishi sara da addar dake hannunsa, kuma ya same shi a hannu.

Kakakin ’yan sanda a Jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya shaida wa manema labarai a yayin gabatar da matashin cewa, bayan samun labarin abin da ya faru suka yi nasara kama ake zargi da saran kanen mahaifin nasa, kuma bayan sun gama bincike za su tura shi zuwa kotu domin yanke  mishi hukunci.