Matashin da ya yi yunkurin fashi a coci ya shiga hannu
Rundunar ‘yan sandar jihar Legas tayi nasarar kame wani matashi mai shekaru 19 da laifin yunkurin yin fashi a coci. Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Legas DSP Bala Elkana, ya shaidawa Aminiya cewa a ranar Asabar din da ta gabata ne mabiya cocin katolika da ke yankin Jakande a Legas ne, suka an […]
Rundunar ‘yan sandar jihar Legas tayi nasarar kame wani matashi mai shekaru 19 da laifin yunkurin yin fashi a coci.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Legas DSP Bala Elkana, ya shaidawa Aminiya cewa a ranar Asabar din da ta gabata ne mabiya cocin katolika da ke yankin Jakande a Legas ne, suka an karar da rundunar cewa, wasu mutum uku akan babur sun shigo filin mujami’ar da mabiyanta ke yin bauta na kwanaki uku inda suka yunkurin sace masu kayayyakin su da suka hadar da wayoyin salula da kudi.
Ya ce, rundunar tayi nasarar kame madugun wadanda ake zargin mai suna Wasiu Kamarudeen, wanda aka same shi da bindiga kirar gida da alburusai an kuma kame babur din su.
Bala Elkana, ya ce rundunar na kokarin kame ragowar ‘yan fashi da suka tsare.