Matashin da ya yi yunkurin yin tsafi da mahaifinsa ya shiga hannnu
Wani matashi dan shekara 26 mai suna Chukwuemeka Okafor, ya shiga komar yan sanda saboda ana zarginsa da yin amfani da shafin sada zumunta na Facebook domin halaka mahaifinsa da kannensa biyu. Aminiya ta binciko cewa lamarin ya faru ne a kauyen Ifite-Awka da ke Jihar Anambra. Matashin ya shaida wa ’yan sanda cewa, ya […]
Wani matashi dan shekara 26 mai suna Chukwuemeka Okafor, ya shiga komar yan sanda saboda ana zarginsa da yin amfani da shafin sada zumunta na Facebook domin halaka mahaifinsa da kannensa biyu.
Aminiya ta binciko cewa lamarin ya faru ne a kauyen Ifite-Awka da ke Jihar Anambra. Matashin ya shaida wa ’yan sanda cewa, ya saka hotunan mutanen ne a shafinsa, inda ya hada baki da wasu abokansa su biyar, domin mika su wajen boka da zai yi tsafi da su.
Wanda ake zargi, kafin asirinsa ya tonu, an bayyana cewa sai da ya lallabi mahaifinsa ya ba shi Naira dubu 100 da nufin zai yi kasuwanci amma a karshe sai ya tafi wajen bokaye tare da rakiyar abokansa, inda ya mika sunan mahaifinsa da kannensa.
Okafor ya bayyana wa ’yan sanda cewa ya tsinci kansa cikin wannan hali ne bayan da wani abokin huldar kasuwancinsa ya damfare shi Naira dubu 400 da nufin za su tafi kasar Dubai kasuwanci, a karshe ya nemi abokin nasa ya rasa. Daga baya “na je na samu wani abokina kuma mai suna Zaki na fada masa damuwata, na ce ina cikin matsala, shi kuma ya ce mini idan ina son yin arziki dare daya akwai sharudda amma fa kada in kuskura in fada wa kowa sirrin, idan na fada zan mutu. Don haka sai ya ce mu kulla hulda ta shafin sada zumunta na Facebook, daga nan sai na sanya hoton babana da na kannena a shafina.”
Da yake yi wa manema labarai karin bayani game da wanda ake zargin, Kwamishinan ’yan sanda a Jihar Anambra, Garba Umar ya ce: “A bayanin da wanda ake zargi ya yi, ya ce hakika ya aikata laifin kuma mahaifinsa bai san cewa kudin da ya amsa wurinsa boka ya ba ba, domin a kashe.