Matashin Da Zaman Gidan Yari Ya Zame Wa Alheri
Matashin da ya koyi sana’a a gidan yari ya koya wa mutum 11 bayan wata hudu da fitowarsa
Wani matashi mai suna Zakariyya Mohammed wanda aka taba daurewa a gidan yari a Gombe ya ce hakan ya zame masa alheri, domin a can ya koyo sana’ar da a yanzu yake dogaro da kansa.
Zakariyya, wanda ya koyi sana’ar hada takalma da jakunkuna a gidan yari ya ce yanzu rayuwarsa ta canja domin ya zama mutum na gari, mai dogaro da kansa kuma a kullum yana iya samun ribar N5,000 zuwa N7,000 daga takalman da hada ya sayar da kuma gyaran da ya yi wa mutane
Matashin, wanda a watan Yuni aka sako shi daga Gidan Yarin Billiri da ke Jihar Gombe, ya ce yanzu ya mallaki shagon kansa, kuma cikin wata hudu bayan fitowar tasa ya koya wa mune 11 sana’ar.
Zakariyya ya ce yana sayar da takalman da ya hada a kan Naira 1,000 zuwa 3,000, jaka kuma daga N700 zuwa N2500 — ya danganci irinta.
- Kotun Ƙoli: Kwankwaso ya jagoranci addu’ar roƙa wa Abba nasara
- Ta antaya wa mijinta ruwan zafi saboda ya ki zuwa biki da ita
Bayan haka, gyara da dinkin takalman da yake yi na kawo masa karin kudade sosai, wanda hakan ya sa ya fara yin adashe don ganin kudin sun yi auki.
Yadda na koyi sana’a a gidan hari —Zakariyya
Zakariyya ya ce kasancewar ba shi da sana’a kafin shigarsa kurkuku ta sa yake ganin shigarsa gidan yarin a matsayin alheri ta rayuwarsa, domin kuwa, a can ya koyo sana’ar da yanzu ta zame masa abin dogaro da kansa.
Da yake labarta wa Aminiya yadda ya fara koyon sana’ar, ya ce, “Wata rana sai Mista Christopher Jen, wanda tsohon Mukaddashin Kwanturolan kuma Mai Kula da Gidan Gyaran Hali da ke garin Biliri, ya same ni ya karfafa min gwiwar cewa na kwantar da hankalina na koyi daya daga cikin sana’oin da ake koyarwa a gidan.”
Zakari ya ce daga nan ne ya fara tunanin koyon sana’ar hada takalma.
Ya ce hada takalma ya fara koya, daga bisani sai ya sake komawa ya koyi yadda ake yin jakukkuna na mata.
Matashin ya ce ya shafe shekara biyu da wata shida a kurkuku kafin a sako shi a watan Yunin shekarar nan ta 2023.
Zakari ya cewa daga fitowarsa zuwa yanzu ya mallaki shagonsa da yake cin gashin kansa, har da masu aiki a karkashinsa.
Ya bayyana cewa bayan fitowarsa ne ya sanar da ’yan uwansa cewa ya koyi sana’a, shi ne suka yi masa karo-karo suka bude masa shagon.
A cewarsa, daga bude shagonsa zuwa yanzu, ya koya wa yara 11 sana’ar kyauta, a cikin watani hudu.
Sannan sai ya yi godiya ga Gwamnatin tarayya da ta bullo da shirin koya wa fursunoni sana’o’i domin kyautata rayuwarsu bayan sun fito.
Daga nan sai ya yi roko a dinga samar wa wadanda suka kammala zaman gidan gyaran halin suka iya sana’a jari da shago na kansu domin kada su koma gidan jiya.
“Hakan zai sa a rage yawan aikata barna ko ta’ammali da miyagun kwayoyi, yanzu ni na zama mai sana’a wanda ba na tunanin sake aikata wani laifi, tunanina a kullum ya za a yi na samu karin kwastomomi” in ji shi.