Matashiya mai yi wa kasa hidima ta mutu a Gombe
Wasu matasa 2 kuma za su maimaita a Jihar
Wata matashiya mai yi wa kasa hidima ta mutu tana tsaka da hidimta wa kasar a Jihar Gombe, kamar yadda Hukumar da ke Kula da matasan ta NYSC ta bayyana.
Hukumar ta kuma ce wasu matasa 2 za su maimaita sakamakon karya dokar da suka yi.
- Majalisar Gombe ta amince Gwamna ya nada mashawarta 30, ya kara wa Ciyamomi wa’adi
- Bin diddigi: Shin da gaske an bude bodar Legas don shigo da motoci?
Ko’odinetan hukumar a Jihar, Dawut Jidda ne ya bayyana hakan a lokacin bikin yaye matasan rukunin B kashi na biyu na shekarar 2023.
Jidda, ya ce an kara wa matasa 2 wa’adin hidimta wa kasar ne sakamakon samun su da laifuffuka bayan sun fuskanci kwamitin ladabtarwa.
Ko’odinetan ya kuma jinjina wa matasan da suka kammala yi wa kasar hidima wajen gudanar da ayyakan al’umma.
Ya kuma hore su da su tsaya kan sana’o’in da suka koya a lokacin yi wa kasa hidima domin samun aikin gwamnati babu tabbas.
“Batun cewa ka gama karatu ka shiga neman aiki ba lallai ba ne ka samu domin an yi wa gwamnati yawa, yafi kyau ka dogara da sana’ar da ka koya,” in ji shi.
Daga nan sai Ko’odinetan ya hore su da su guji shiga ayyakan masha’a don kare kansu daga fadawa fushin hukuma.