Matashiya ta ƙirƙiri manhajar fassara kukan yara
Khatib Layali ita ce ta kirkiri wannan manhaja ta kuma sa mata suna ‘Kulawar uwa’ ko ‘Mother care’ da Turanci.
Kasancewar jariri ba ya da bakin yin magana, yana bayyana buƙatarsa ce ko nuna damuwarsa tare da neman dauki ta hanyar kuka.
Kuma babu wata hanya ta gane abin jaririn yake so ko yake ki ta wannan hanya ta kuka.
- Boko Haram ta yi wa manoma 13 yankan rago a Borno
- Tinubu zai yanke hukuncin karshe kan jirgin Nigeria Air —Keyamo
Sai dai wata budurwa ta yi kokarin magance wannan matsala ta hanyar gano abin da yara kanana da ba su da baki ke nufi idan suna yi kuka.
Wannan fasihiyar budurwa ta yi wannan kokari ne ta hanyar ƙirƙiro wata manhaja wacce za a iya saukewa a wayar hannu idan yaro yana kuka manhajar za ta fassara kukan yaron tare da rubuta damuwarsa ko abin da yake so.
Khatib Layali ita ce ta ƙirƙiri wannan manhaja ta kuma sa mata suna ‘Kulawar uwa’ ko ‘Mother care’ da Turanci.
Budurwar ta ce ta ƙirƙiri manhajjar ce domin ta taimaka wa mahaifiyarta fahimtar abin da kannenta tagwaye ke so daga koke-kokensu.
Amma tun da kannen nata ’yan biyu sun girma kuma har sun soma magana, yanzu suna amfani da manhajjar kan karamin kanensu da ake goyo a gidan.
Kuma ana amfani da manhajar don fahimtar yunwa ke damun jariri ko so yake ya yi barci ko ciwon jiki ko kuma akwai famfas din ya jike yana bukatar a canza masa duk daga koke-kokensa.
Amfani da manhjar ba ya da wuya da zarar mutum ya sauke ta a wayar kawai kunnawa mai shi zai yi sannan ya bude abin maganar manhajar ya sa abin maganar wayarsa ya dauki sautin kukan jaririn.
Manhajar za ta nadin sautin kukan yaro sannan ta sarrafa a irin nata yaren da sabuwar fasahar Artificial Intellegience (AI) ta fitar da abin da jaririn yake so.
Khatib ta ce manjahar na aiki da kashi 93 cikin 100 babu kuskure, ta kuma yi niyyar yada mahajar a duniya domin iyaye mata su amfana.
Ta ce burinta na gaba shi ne ta kirkiro wata manhajar da za ta gano masu cutar laka (autisms).
Khatib ’yar asalin kasar Falasdinu ce da a yanzu kasar tasu take fama da hare-haren sojin Isra’ila.
Shin yaya wannan burin nata zai kasance? Lokaci ne kawai zai nuna.