Matashiya ta caka wa wata mata kwalba

Wata mata ’yar shekara 28, ta gurfana a gaban kotu bisa zargin caka wa wata kwalba tare da yi mata mummunar illa.

Matashiya ta caka wa wata mata kwalba

Fasasshiyar kwalba

Wata mata ’yar shekara 28 ta gurfana a gaban kotu bisa zargin caka wa wata mata kwalba tare da yi mata mummunar illa.

Dan sanda mai shigar da kara, ASP, Christian Okonofua, ya shaida wa kotun cewa wadda ake kara ta fasa kwalbar giya sannan ta caka wa mai karar mai suna Misis Kemi Oseni,  ta yi mata rauni.

An gurfanar da ita ne a gaban wata kotun majistare da ke Ikorodu a Jihar Legas, bisa tuhume-tuhume biyu, amma ta ki amsa laifin.

Dan sandan ya sanar da kotun sanar da kotun cewa an aikata laifin ne a ranar 24 ga watan Mayu, da misalin karfe 10:30 na safe, a unguwar Ikorodu.

A cewar mai gabatar da kara, laifukan sun ci karo da sashe na 168(d) da na 245 na dokar laifuka ta jihar Legas, na shekarar 2015.

Majistare A.O. Onalaja ya bayar da belin wadda ake kara a kan kudi N200,000, tare da mutane biyu masu tsaya mata.

Onalaja ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 13 ga watan Yuni, 2024.