Matashiya ta huda tsaunuka don yi wa kauyensu hanya a Sin
Mazaunan kauyen Mahuai da ke garin Luodian a Kudu maso Yammacin kasar Sin da ke Gundumar Guizhou, Tsaunuka sun killace su daga shigowa cikin al’umma a sauran sassan fadin kasar. Don haka wata matashiya mai suna Deng Yingdiang ta jagoranci wasu ’yan uwanta suka yi ta haka da saran duwatsu, ta hanyar amfani da guduma […]
Mazaunan kauyen Mahuai da ke garin Luodian a Kudu maso Yammacin kasar Sin da ke Gundumar Guizhou, Tsaunuka sun killace su daga shigowa cikin al’umma a sauran sassan fadin kasar. Don haka wata matashiya mai suna Deng Yingdiang ta jagoranci wasu ’yan uwanta suka yi ta haka da saran duwatsu, ta hanyar amfani da guduma da sauran kayan aiki na gargajiya, har suka samu yin hanya mai nisan mita 200.
Wannan aiki na su ya biya bukata domin an samu hanyar shige da fice daga kauyen. Duniya kuma ta gan su
A halin yanzu ana matukar girmama wannan matashiya Deng Yingdiang, muisamman saboda jajircewarta da karfin hali, har ta cimma wannan burin a samar da hanyar da za ta danganta kauyen su da sauran sassan kasar.