Matashiya ta zama tsohuwar kwana guda

Wata matashiya ’yar shekara 29 da ke Shenzhen a kasar Sin, ta sauya kamanunta, inda ta zama tsohuwa, ta kwatanta rayuwar tsofaffi, ta shiga cikin su har na tsawon kwana guda. Ta kuma yi hakan ne, domin ta dandana irin rayuwar tsofaffi, musamman  jin ta damfaru da son ta san yadda rayuwarta za ta kasance […]

Matashiya ta zama tsohuwar kwana guda
Matashiya ta zama tsohuwar kwana guda

Wata matashiya ’yar shekara 29 da ke Shenzhen a kasar Sin, ta sauya kamanunta, inda ta zama tsohuwa, ta kwatanta rayuwar tsofaffi, ta shiga cikin su har na tsawon kwana guda. Ta kuma yi hakan ne, domin ta dandana irin rayuwar tsofaffi, musamman  jin ta damfaru da son ta san yadda rayuwarta za ta kasance idan ta tsufa.
A rayuwar tsofaffi ta kwana guda da ta kwatanta, wannan matashiya ta yi kokarin shiga cikin tsofaffi, ta yi wasan Mahjong (kwadon mutanen Sin) da mkwaftanta tsofaffi. Don ta tabbatar ta kwatanta irin wannan rayuwa, sai ta rika yin aikace-aikacen gidanta yadda tsofaffi ke gudanarwa da kan su. Ta je kasuwa da wurin sayar da magani, sannan ta tsaya ta huta a hanya.
A cewar Fenga, lokacin da ta zauna a kan benci, sai ta ji kadaici da gajiya sun kamata, saboda mafi yawancin tsofaffin da take tare da su, sun koma kofar gidan su, sun tare a can.
A kasar Sin mutane (musamman matasa) na barin iyayen su masu nisan shekaru, su kadai a gida, su kuma su nausa zuwa birane don neman ayyukan yi. Matasan na tafiya ne zuwa biranen Beijing da Shangai da Guangzhou. Saboda dimbin ayyukan da ake gudanarwa a wadannan birane, mutane da dama bas a samun damar komawa gida, har tsawon shekara ko a lokutan bukukuwabn shekara da hutu.
A ruwayar wata cibiyar nazarin iyali ta kasar Sin (Chinese Family Debelopment), ta bayyana a rahoton ta na shekarar 2015, cewa, tsofaffin mutane a kasar Sin su kadai ke rayuwa da daukar dawainiyar kan su, har ta kai ga ana yi musu lakabi da “masu zaman kadaici.”