Matashiya TV ta horar da matasa sama da 3,000 sana’o’i da aikin jarida a Kano
An buƙaci waɗanda suka samu horon da su yi amfani da ilimin da suka samu wajen dogaro da kansu.
Tashar Matashiya TV na ci gaba da horas da matasa a fannoni daban-daban domin ƙarfafa musu gwiwa su dogara da kansu da kuma rage zaman kashe wando a Jihar Kano.
Tashar na bai wa matasa horo a fannonin aikin jarida, tace sauti, tace bidiyo, da ɗaukar hoto da bidiyo, domin inganta ƙwarewarsu a harkar yaɗa labarai.
- Sojoji sun kashe mai yaɗa farfagandar ISWAP da tawagarsa a Borno
- An tsinci gawar wani tsoho a otal a Jigawa
Baya ga haka, Matashiya TV ta kuma fara horas da matasa sana’o’in dogaro da kai da suka haɗa da na’urorin samar da wutar lantarki na hasken rana, da kuma haɗa sinadaran wankin mota, Shamfo, Izal domin dogaro da kai.
Mamallakin Matashiya TV, Abubakar Murtala Ibrahim, ya ce wannan shi ne karo na biyu da ake gudanar da irin wannan horarwa a shekarar 2026.
A cewarsa, a zagayen farko an horas da matasa 67 kan girka na’urorin hasken rana, yayin da mata 32 suka samu horo kan haɗa Shampoo, Shower Gel, Sinadarin wanke mota da Izal.
Ya ƙara da cewa ba wannan ne karo na farko da Matashiya TV ke shirya irin wannan shiri ba.
Ya ce tun shekarar 2016 tashar ke horas da matasa sana’o’in dogaro da kai tare da bai wa ‘yan jarida horo domin haɓaka ƙwarewarsu.
Abubakar, ya bayyana cewa sama da matasa 3,000 ne suka amfana da shirye-shiryen horaswar da Matashiya TV ta gudanar tun daga shekarar 2016 zuwa yanzu.
Ya ce manufar shirin ita ce taimaka wa matasa su dogara da kansu, su daina jiran aikin gwamnati, tare da rage zaman kashe wando.
A cewarsa, shirin ya fara haifar da sakamako mai kyau, domin a yanzu ana samun sabbin kafafen yaɗa labarai masu zaman kansu da dama.
Ya buƙaci waɗanda suka samu horon da su ci gaba da amfani da ilimin da suka koya domin inganta rayuwarsu.
Haka kuma, ya yi kira ga matasan da ke jiran aikin gwamnati da su rungumi sana’o’in dogaro da kai.
Ana sa ran kammala zagaye na biyu da na uku na horaswar a watan Satumba, kafin a gudanar da bikin yaye waɗanda suka ci gajiyar shirin a watan Oktoba.