Matashiya: Waiwaye adon tafiya
Jama’a suna murna da kuma maraba da shirin da aka ce Gwamnatin Tarayya na yi na maido da tsarin yaki da rashin da’a, wanda a Turance ake kira War Against Indiscipline, ko kuwa WAI a takaice. Wannan tsari zai zame siga ne irin wancan na farko da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta tsira sa’ilin da […]
Jama’a suna murna da kuma maraba da shirin da aka ce Gwamnatin Tarayya na yi na maido da tsarin yaki da rashin da’a, wanda a Turance ake kira War Against Indiscipline, ko kuwa WAI a takaice. Wannan tsari zai zame siga ne irin wancan na farko da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta tsira sa’ilin da yake shugabancin gwamnatin mulkin soja, shekaru 32 da suka shude.
Labudda manyan jami’an gwamnati na sane da ayyukan da suka jibancii wayar da kawunan jama’a da kuma janyo hankulansu game da take-taken gwamnati da kuma fahimtar da su manufofin da take bullowa da su, shi ya sa suke son ganin sabon shirin sake gabatar da Yaki da Rashin da’a zai samar da rundunar dakarun da za a kira WAI Brirgade, wacce za a dora wa hakkin samar da wasu muhimman bayanan da za su taimaka wa mahukunta daidaita al’ummomi bisa tafarkin da ya dace da bin doka da oda da kuma girmama ka’idoji da aiki da su, daidai da ikirarin canjin da wannan gwamnatin ke yi a halin yanzu.
A watan Janairun da ya gabata ne Ma’aikatar Yada Labarai ta Tarayya, wacce ko a karon farko na gabatar da tsarin Yaki da Rashin da’a tana kan gaba, ita ce kuma a wannan karon aka dora wa hakkin sake wani sabon tsari dangane da haka, wanda zai dara na karon farko armashi da kuma biyan bukata. Kamar yadda aka bayyana, makasudin wannan sabon tsarin shi ne fahimtar da kowane dan kasa matsayinsa na kasancewa muhimmin mataki a cikin tsarin yakin da ake yi, saboda haka nan wajibi ne shi da kansa ya gyara kansa, ya kuma tsarkake kansa, kafin ya nemi waninsa ya yi haka. Muddin kowa da kowa zai yaki kansa, ya kuma tabbatar ya fi karfin zuciyarsa, to ba abin da zai hana samun gagarumar nasara wajen murkushe dukkan miyagun dabi’un da ke addabar jama’a, suna kuma hana su zaman lumana a cikin al’umma. Wannan tsarin shi ne ake kira “Change Begins With You.”
Ba makawa, har yanzu akwai masu aikata miyagun dabi’u da bin munanan manufofi birjikl a cikin kasar nan, kuma wadannan abubuwan kyamar na nan suna ta wahalshe su, suna kuma janyo wa kasar koma-baya. Za a fahimci haka ne kawai idan aka yi la’akari da halayyar da muke nuna wa a bakin ayyukanmu da yadda muka bar kazanta ta zame a bar kwalliyarmu, muna kwana, muna tashi a cikinta; da kuma yadda ba mu damu da bin doka da oda ba, sa’anan kuma ba ruwanmu da bin ka’idoji ko wasu sharuddan da za a gindaya yayin mu’amala da ‘yanuwanmu.
To, muddin ana son yin gyara a cikin wannan al’amari mai tsananin ban takaici sai fa an tashi haikan wajen wayar da kawunan jama’a ta hanyar yin amfani da dukkan kafafen yada labarai da ake da su, da kuma yadda su shugabanni za su gwada halaye da dabi’un kwarai da mabiya za su yi koyi da su. Dangane da haka tilas ne a bi tafarkin dimokuradiyya, a kuma yi aiki da ka’idojin da ke shimfide bisa wannan turbar. Sau da yawa wadansu kan dauka cewa wai ‘yan Najeriya ba su son gyara halaye ko su canja dabi’unsu, shi ya sa ake gani tunda sun zame tamkar dabbobi sai an hada masu da na-jaki, wanda ke taurin kai, sai an doke shi. Tsumagiya ce kawai za ta fadakar da irin wadannan kangararrun mutanen yayin da ta ratsa gadon bayansu, a lokacin ne za su zabura, su aikata abin da suka ki cikin lalama da lumana. To amma idan aka ga laifin talakan da bai son bin doka sai ya sha duka, sai kuma a ga laifi, ko kuma a ce wautar hukumomin da ba su samar da abubuwan inganta rayuwar talaka ta yadda zai ci gajiyarsu har rayuwarsa ta ingantu.
Yayin da hukumomi za su yi ta turzawa don karfafa zukatan jama’a ta yadda za su amince da bin doka da oda, sai kuma su dukufa wajen samar da wuraren da jama’a za su tsuguna don rage dawa, ko inda za su zagaya don su jika kasa. Akwai wani maganin matsuwa ga dan-adan da ke son rabuwa da wata lalura, ido rufe illa kawai ya samu wurin da zai zukku ce matsalarsa cikin sauki da rufin asiri? Idan babu irin wannan wuri, ko ina ya samu sai ya zagaya, ya faki idanuwan jama’a, ya rage tsawo, ya bata wuri, ya yi tafiyarsa abinsa.
Haka nan ma karancin motocin haya, manya da kanana da kuma rashin garewani ko manya-manyan bokitan tara juji a gefen hanya da kuma kananan kwandunan da za a jefa guntuwar takardar tsiren da aka canye , ko bawon raken da aka tsotse da kuma bawon gyadar da aka bare, aka bushe, aka lakwame, a ofishoshi da makarantu da asibitoci da kuma cikin motocin haya, abubuwa ne da ke karfafa zukatan jama’a wajen karya doka da ka’idar tsabtace muhalli, kuma dole ne a kiyaye haka.
A wancan shirin Yaki da Rashin ka’a, karo na farko, an bullo da tsarin bin layi yayin gudanar da al’amura, aka haramta yin rige-rige a ko’ina. Hakan kuma ya biya bukata, domin an bar yin turereniya, ba a ruguntsumi, sa’anan kuma ba wanda ke daka-wawa wajen rabon kayayyakin masarufi ko na abinci. A yanzu kuma idan ana so a koma ga haka, wajibi ne a yi amfani da manufofi da tsare-tsaren da suke bisa tafarkin dimokuradiyya, a kuma guji tursasa wa kowa, amma a tabbatar an nuna masa illolin kauce wa kaidoji, ya kuma fahimci haka.
To amma sai dai ba za a cimma wata kwakkwarar nasara ba a kokarin sake dawo da Yaki da Rashin da’a muddin ba an tashi haikan ne ba wajen fadakar da jama’a game da haka, sa’annan kuma wadanda za su dukufa yadin tilas ne su zame jaruman da suka yaki nasu zukatan, suka kuma murkushe su, domin kuwa babu wani jan gwarzo a duniyar nan face wanda ya yi galaba kan zuciyarsa, ya daure, ya hana ta aikata abin da take so, wanda ya saba shari’a’. To irin su ne za a dora wa hakkin ilmantar da jama’a game da muhimmanci danne zuciya da hana ta aikata abin da take so, su kuma nuna wa jama’a yiwuwar fadawar su cikin kunci da wahala idan suka kauce hanya, ko suka karya wata doka da ka’ida. Ta haka ne za su ji dadin gudanar da ayyukansu, amma fa sai idan sun kasance kamilallu, masu cikkaken hankulan da za su bambanta su daga dabbobin da ake kiwo. Muna maraba da zuwan yaki da rashin da’a karo na biyu, da fatan za a yi ta waiwayen abubuwan da suka faru a baya da niyyar yi wa tafiyar da za a yi kyakkyawan ado. An dai ce tuana baya shi ne roko.