Matata ce a gado na bakwai

Wasu maza uku aka kai matansu asibiti wajen haihuwa, daya an kwantar da matarsa a gado na biyu daya a gado na uku, dayan kuma agado na bakwai. Suna zaman jira sai Nas ta zo ta ce wane ne matarsa ke gado na biyu? Sai ya ce “ga ni.” Sai ta ce “Ka yi murna […]

Matata ce a gado na bakwai
Matata ce a gado na bakwai

Wasu maza uku aka kai matansu asibiti wajen haihuwa, daya an kwantar da matarsa a gado na biyu daya a gado na uku, dayan kuma agado na bakwai. Suna zaman jira sai Nas ta zo ta ce wane ne matarsa ke gado na biyu? Sai ya ce “ga ni.” Sai ta ce “Ka yi murna matarka ta haifi ’yan biyu!” Can aka ce “Ina wanda matarsa ke gado na uku?” Ya ce “ga ni” Sai aka ce matarka ta haifi ’yan uku. Wanda matarsa ke gado na bakwai sai ya fashe da kuka. Nas ta ce, “kukan me kake yi Malam?” Sai ya ce, “Matata ce a gado na bakwai!” Wato yana tsoron kada a ce masa ta haifi ’yan bakwai. Daga 09092969381 Top of Form Bottom of Form