“Matata da ’ya’yana na cikin wadanda aka kama a Abiya”
Malam Salihu Usman, wani daga cikin mazauna birnin Fatakwal ne, wanda kamun da jami’an tsaro suka yi wa mutane 486 a Jihar Abiya kwanakin baya, ya rutsa da matarsa da ’ya’yansu uku mata. Aminiya ta tattauna da shi ta wayar salula, inda ya bayyana damuwar da yake ciki: Aminiya: Yaya sunan malamin?Sunana Salihu Usman. Ina […]

Malam Salihu Usman, wani daga cikin mazauna birnin Fatakwal ne, wanda kamun da jami’an tsaro suka yi wa mutane 486 a Jihar Abiya kwanakin baya, ya rutsa da matarsa da ’ya’yansu uku mata. Aminiya ta tattauna da shi ta wayar salula, inda ya bayyana damuwar da yake ciki:
Aminiya: Yaya sunan malamin?
Sunana Salihu Usman. Ina sana’ar sayar da kankana a garin Fatakwal.
Aminiya: Kana zaune a ina ne yanzu?
Ina zaune a garin Fatakwal, ni da iyalina.
Aminiya: Gaskiya ne matarka da ’ya’yanka suna cikin mutane 486 da jami’an tsaro suka kama kwanakin baya a Jihar Abiya?
Matana biyu, sai daya da ke zaune a Taura, Jihar Jigawa ta haihu, shi ne kishiyarta ta je can bikin suna, suna kan hanyar dawowa, sai wannan al’amarin ya rutsa da su.
Aminiya: Uwargidan ce ta haihu ko amarya?
Amaryata ce da ke zaune a Jihar Jigawa ta haihu, sai uwargidana ta je wurinta bikin sunan.
Aminiya: Ita kadai aka kama ko har da ’ya’yanta?
Ita da ’ya’yanta uku ne. Mata ne dukkansu.
Aminiya: Za su kai kamar shekara nawa?
Ta farko ’yar shekara kusan 9 ce, sai ’yar shekara 6, sai kuma ’yar shekara 2.
Aminiya: Ka yi kokarin bincike don sanin halin da suke ciki?
Na yi bakin kokarina don in gan su, kasancewar na je wurin da aka tsare su, amma an hana ni ganin su. A matsayina na talaka, baya ga haka ni ba mai sarauta ba ne, sai aka hana ni ganinsu. Na je, amma iya bakin get aka tsare mu. Suka ce mana babu halin da za su bar mu mu shiga mu ga wadannan ’yan uwanmu da aka tsare din. Na je wurin sau uku, amma har yanzu ba a bar ni na gan su ba.
Aminiya: Kana da labarin halin da suke ciki?
Matsayin da ake ciki yanzu shi ne, ban gan su ba, ban yi waya da su ba, ba zan iya sanin halin da suke ciki ba. Don haka babu kowane irin labarin da zan bayar a kan su. Babu abin da muke yi yanzu da ya wuce addu’a, duk abin da aka ce ba ka gani ba, ba ka kuma ji ba, to yaya za ka yi da shi? Domin sai ka kira mutum zai sanar da kai halin da yake ciki. Sai ka ga mutum za ka iya gane halin da yake ciki, ko da bai yi magana ba. Hakan ya sa muke ci gaba da addu’a.
Aminiya: Yaya ka ji da aka ce maka an kama matarka da ’ya’yanka bisa zargin Boko Haram?
Ba ’yan Boko Haram ba ne, matar aure ce da nake tare da ita shekara 12, babu inda ta sani, ba ta san wani abu Boko Haram ba. Ni ma mijinta ban san wani abu Boko Haram ba, ballantana ita da kuma kananan yara mata.
Aminiya: Gwamnatin Jihar Kano ta tura wani kwamiti don ya tantance ’yan asalin Jihar Kano, ko Gwamnatin Jihar Jigawa ta yi wani kokari dangane da ku ’yan jiharta?
A halin da muke ciki na talakawa, idan gwamnati ta yanke daukar wani hukunci, talaka ba zai sani ba, yakan san hukunci ko matakin da gwamnati ta dauka ne a wurin irinku, wato a gidajen rediyo ko jaridu. Don haka a matsayinmu na talakawa, gwamnati ta yi magana da mu ma ai ba ta taso ba.
Aminiya: Yanzu a wane hali kuke ciki? Shin ba ku fuskantar wata barazana?
A halin yanzu babu wata barazana da muke fuskanta daga abokan zamanmu da Allah Ya hada mu, wato Kiristoci. Babu wadansu damuwowi da suke tasowa, babu kuma alamar wata damuwa. Har yanzu dai ban ji wani korafi daga rukuninmu na talakawa, wadanda suka kama daga Musulminmu har zuwa Kirista ba.
Aminiya: Shin har yanzu ’yan Arewa na ci gaba da zuwa Kudu?
Har yanzu mutane suna ci gaba da kaiwa da komowa, sai dai idan irin hakan ya faru jikin mutane zai yi sanyi. Kowa na zaman dar-dar.
Aminiya: Ba ka ganin ya kamata a ce ’yan Arewa sun daina zuwa ci-rani Kudu, musamman dangane da irin wannan matakin da ake dauka a kan ’yan Arewa?
A nawa ganin babu abin da ya fi mana sauki face mu kama addu’a. Talaka a Najeriya ba shi da abin da ya wuce addu’a, kuma a nawa tunanin addu’ar ita ce mafita. Aminiya: Mun samu labarin akwai wanda ya yi aure za a kawo masa amaryar, sai aka kama ta har da ’yan rakiyarta, kana da labarin faruwar hakan?
Ban san mutumin ba, amma ina da labarin lallai akwai mutumin da ya yi aure, inda aka kama amaryar tasa da kuma ’yan rakiyarta.
BBC ta tuntubi Mista Mike Omori, Shugaban Cibiyar Samar da Bayanai Kan Tsaro ta Najeriya kan ci gaba da tsare mutanen da ake yi, sai ya ce, “Muna kan bincike. Rokon da muke so mu yi wa malaman addinai na Musulmi da Kirista shi ne, su yi shiru su ba jami’an tsaro damar yin bincike don a samar da tsaro a kasar nan. Wadannan surutai da ake ta yi, ba za su taimaka wajen binciken da ake yi ba. Wannan ba yaki da addinin wani ba ne; ba yaki da wani mutum ko kungiya ko kuma sashen kasar Najeriya ba ne”.