Matata ta san ni Musulmi ne kafin in aure ta – Makun

Mista Makun Iluobe Emarie mutumin da matarsa Mary Akinola Jacob Makun ta yi kararsa a Babbar Kotun Jihar Bauchi cewa ya yi mata karyar shi Kirista ne kafin ya aure ta ya musanta haka, inda ya ce matar tasa ta san shi Musulmi ne kafin su yi aure. Mary Akinola Jacob Makun ta gurfanar da […]

Matata ta san ni Musulmi ne kafin in aure ta – Makun

Mista Makun Iluobe Emarie mutumin da matarsa Mary Akinola Jacob Makun ta yi kararsa a Babbar Kotun Jihar Bauchi cewa ya yi mata karyar shi Kirista ne kafin ya aure ta ya musanta haka, inda ya ce matar tasa ta san shi Musulmi ne kafin su yi aure.

Mary Akinola Jacob Makun ta gurfanar da mijinta ne a gaban Mai Shari’a Aliyu Baba Usman ne cewa mijin ya yi mata karyar cewa shi Kirista ne kafin ya aure ta, amma bayan sun yi aure sai ya ce mata shi Musulmi ne zai iya auren mata hudu.

Mista Makun ya ce bai yi mata karya ba, illa dai sun yi haka ne (shi da ita) domin iyayenta da limamin majami’arsu su yarda da shi a daura musu aure.

Bayanin haka na kunshe ne a cikin takardar kariya da suka gabatar a gaban kotun shi da wadda ake kara ta biyu da take zargin zai aura mai suna Chinenneye Joy Ewunife.

Ya ce tun farko ya shaida wa mai karar cewa shi Musulmi ne, sai ta ce ya yi kamar ya bar addininsa domin ya aure ta saboda a cewarta ta haka ne kawai limamin majami’arsu da iyayenta za su yarda da shi, kuma har suka yi auren da alkawari a tsakaninsu cewa ba zai bar addininsa na Musulunci ba, suna ma yin bukuwan Sallah ita ma tana gayyatar ’yan uwa da abokanta su zo gidan su ci abincin Sallah.

Ya ce duk wani alkawari da suka dauka da mai karar ya cika, cewa ba zai auri wata mata ba, bai aura ba, haka cewa zai biya mata kudin makaranta ya cika, duk da ta yi kokarin ganin an samu tangarda bayan dimbin kudin da ya kashe a shekarar 2015 da 2016.

Mista Makun ya ce bai taba daga hannu ya bugi matarsa ba balle ya ji mata rauni, kuma karya ta yi da ta ce ya yi mata fatan mutuwa. Ya ce bai san ba ta da lafiya ba, illa ta ce za ta je taron majami’arsu a Abuja, kuma ta dawo tsakar dare tana buga kofa shi kuma ya ji tsoron fitowa saboda ’yan fashi kan yi amfani da wani su sa ya kira ka, kana bude kofa su far maka. Ya ce bai san za ta dawo ba, amma lokacin da ya gamsu cewa matarsa ce ta dawo da tsakar dare sai ya bude mata kofar.

Mista Makun ya ce matarsa ta yi ta yi masa barazanar za ta kashe shi, kuma lokacin da ya ga ta canja halayenta ya shawarce ta ta gyara don su zauna lafiya tunda ga shi da haihuwa a tsakaninsu amma ta ki. Ya ce saboda fitinarta ta yi yawa don a samu zaman lafiya ya sa ya bar gidan, kuma duk da haka shi ke ba ta kudin abinci da na bukatun yau da kullum.

Ya musanta komawa gidan wacce take kara ta biyu da kwana, ya ce ba wata soyayya a tsakaninsu. Ya ce ya koma wani gida ne a Unguwar GRA ba gidan wacce ake kara ta biyu ba. Kuma ya ce ya tura mata sako ta waya ne saboda ta tura masa sakon cewa za ta kashe shi, don haka ba zai iya ci gaba da zama da ita ba.

Mista Makun ya bukaci kotun ta sa ta ba shi dansa kuma ta dawo da dukan kayayyakin da ta cire a gidan. Idan kuma kotu ta ce a ba ta kula da dan to a gindaya sharadin za ta kula da shi sosai, kuma zai rika ba ta Naira dubu 30 a wata, zai biya kudin makaranta da na jinyar dan da sharadin ba za ta sake sa wa wata ko wani ya dauke shi zuwa wani wuri kamar yadda ya yi zargin ta sa wata ta dauke shi zuwa Kano ba, tare da barin dan ya rika zama a wurinsa a ranakun Asabar da Lahadi da lokacin da yara suke hutun makaranta.

Wadda ake kara ta biyu Chinenneye Joy Ewunife ta karyata zargin cewa suna soyayya da Makun, inda ta ce mai karar ta kitsa labarin ne da gangan domin neman kotun ta tausaya mata.

Idan za a tuna Mary ta yi karar Makun ne tana bukatar kotun ta raba aurensu domin ta samu shaidar da za ta yi wani aure, sannan kotun ta ba ta ikon kula da dan da suka haifa kuma ta sa mijin nata ya rika ba ta Naira dubu 150, don kula da dan kowane wata. Kuma ya biya ta kudin ilimantar da dan kuma kotu ta sa ya biya ta Naira dubu 300 domin bata mata rai da suka yi.

Mai shari’a Aliyu Baba Usman ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 13 ga Satumba mai zuwa.