Matata ta taɓa kawo min ƙarar Akpabio — Mijin Natasha
Mijin Natasha ya ce da kansa ya taɓa tunkarar Akpabio kan cin zarafin da ya mata a baya.

Mijin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, Emmanuel Oritsejolomi Uduaghan, ya bayyana cewa matarsa ta taɓa kawo masa ƙorafi game da cin zarafin da ta ce Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya yi mata.
A cewarsa, rikicin ya fara tun lokacin da Natasha ta tsaya takarar kujerar Sanata a 2019 a ƙarƙashin jam’iyyar SDP, inda ta nemi kujerar Sanatan Kogi ta Tsakiya.
A lokacin, Akpabio yana riƙe da mukamin Ministan Neja Delta.
“Da kaina na je na same shi na buƙaci ya bai wa matata girman da ta cancanta, sannan ya girmama abotar da ke tsakaninmu.
“Bayan mun tattauna sai muka amince da a warware maganar cikin mutunci,” in ji shi.
Bayan zaɓen 2019, Natasha ta sake tsayawa takarar Sanata a 2023 a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, inda ta samu nasara.
A lokacin, ana raɗe-raɗin cewa Akpabio bai ji daɗin yadda ta samu goyon baya ba, kuma hakan ya ƙara haddasa rashin jituwa a tsakaninsu.
“Amma bayan maganar da muka yi, sai matata ta ci gaba da bayyana damuwa game da irin cin zarafin da ta ke fuskanta daga shugaban majalisar.
“Ni dai na yarda da matata, kuma aure muka yi na soyayya da ƙauna. Babu abin da ya fi min ita a yanzu domin ita ce farin cikina.”
Natasha dai ta ce tana da wasu hujojji da za ta fitar, wanda ke nuna yadda Akpabio ya neme ta, lamarin da yanzu haka ya haifar da zazzafar muhawara a Najeriya.