Matatar Dangote ta dakatar da sayar da fetur a Naira

Matatar ta ce wannan matakin na wucin gadi ne, da zarar ta samu kaya a farashin Naira za ta dawo siyar wa ‘yan Najeriya.

Matatar Dangote ta dakatar da sayar da fetur a Naira

Matatar Dangote ta sanar da dakatar da sayar da Man Fetur da Naira na wucin gadi.

Kamfanin ya bayyana wannan mataki ne a cikin wata sanarwa da ya aike wa dillalan man fetur a ranar Laraba da rana.

A cewar sanarwar, matatar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne domin guje wa matsalar biyan kuɗin ɗanyen mai da ta ke saya da dalar Amurka.

“Ya zuwa yanzu, mun sayar da sama da adadin man fetur da muka samu a Naira.

“Domin daidaita cinikayyarmu da sayen ɗanyen mai, dole ne mu ɗauki wannan mataki na wucin gadi,” in ji sanarwar.

Kamfanin Dangote ya kuma ƙaryata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa ya dakatar da sayar.

Kamfanin ya ce wannan labari ba gaskiya ba ne, inda ya jaddada cewa tsarinsa yana da inganci kuma ba a samu wata matsala ba.

Matatar ta Dangote ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da sayar da mai a Naira da zarar ta samu ɗanyen mai da aka sayar mata a Naira daga kamfanin NNPC.

“Muna nan daram wajen yi wa kasuwar Najeriya hidima, kuma za mu dawo da sayar da mai a Naira da zarar mun samu kaya,” in ji sanarwar.