Matatar Dangote ta dawo sayar da fetur da Naira
Dilallan man fetur sun nuna farin cikinsu na dawo da amfani da Naira a matatar.
Matatar Man Dangote ta dawo sayar da man fetur da Naira bayan dakatar da sayarwa na tsawon mako guda.
Haka kuma, ta ƙara farashin fetur daga Naira 1,075 zuwa Naira 1,215 kan kowace lita, wanda aka samu ƙarin Naira 140 wato kusan kashi 13 cikin 100.
- Trump ya jinjina wa Tinubu kan yaƙi da ta’addanci a Najeriya
- Kano: Ka da ku biya ko ficika don yin auren gata — Hisba
Matatar ta dakatar da sayar da fetur a ranar 15 ga watan Yuli bayan ta fara amfani da dalar Amurka wajen sayar da man da take tacewa.
Aminiya ta gano cewa sabon farashin da Matatar Dangote ta ƙara ya fi arha idan aka kwatanta da farashin fetur da ake shigowa da shi daga ƙasashen waje.
A wasu wuraren, ana sayar da fetur kusan Naira 1,274 kan kowace lita, yayin da wasu gidajen mai a Legas ke sayar da shi sama da Naira 1,300 kan kowace lita.
Sun sanar da kwastomominsu cewa sun koma yi wa tankokin mai lodi, kuma za a ci gaba da sayar da fetur da Naira.
Dakatarwar da aka yi na mako guda ta janyo ƙarancin fetur a wasu sassan ƙasar, lamarin da ya sa farashin ya yi tashin gwauron zabi.
A Jihar Legas, matsakaicin farashin man fetur daga matatar ya tashi daga Naira 1,075 zuwa Naira 1,275 kan kowace lita, sakamakon ƙarin kuɗin da ‘yan kasuwa ke kashewa wajen sayen mai.
A baya, Matatar Dangote ta bayyana cewa ta koma amfani da dalar Amurka ne saboda rashin isasshen ɗanyen mai da take samu ƙarƙashin shirin Gwamnatin Tarayya na musayar Naira da ɗanyen mai.
Shugaban Ƙungiyar Masu Dillancin Man Fetur Mai Zaman Kansu ta Najeriya (IPMAN), Alhaji Abubakar Maigandi, ya ce ya yi matuƙar farin ciki da wannan mataki.
Ya ce mambobin ƙungiyar za su koma lodin fetur nan take, kuma hakan zai taimaka wajen inganta wadatar man fetur a faɗin ƙasar bayan shafe kwanaki ana fama da ƙarancinsa.