Matatar Dangote ta kara farashin fetur zuwa N955
Karin Naira 55 a farashin litar man fetur zai fara aiki ne a ranar Juma’a, kamar yadda matatar ta sanar.
Matatar Man Fetur ta Dangote ta yi wa manyan dillalai karai karin Naira 55 a farashin kowace lita daga N899 zuwa Naira 955.
Karin na zuwa ne bayan Kungiyar Dillalan Man Fetur (IPMAN) ta yi watsi da hasashen tashin farashin man.
A Safiyar Juma’a Matatar ta sanar da karin farashin litar fetur da Naira 55, saboda abin da ta kira tashin farashin danyen mai nau’in Brent a kasuwar duniya.
Sanarwar da matatar ta fitar ta ce, daga yanzu manyan ‘yan kasuwa masu sayen lita miliyan biyu zuwa miliyan 4.99 za su rika sayen litar kan Naira 955, masu sayen lita miliyan biyar zuwa sama kuma a kan Naira 950.
- Hamas za ta sako mutanen da sace a Isra’ila —Netanyahu
- An daure tsohon Fira Ministan Pakistan Imran Khan shekara 14 kan rashawa
- CP Hauwa Ibrahim: Bakanuwar farko da ta zama Kwamishinar ’yan sanda
Masu sayen lita miliyan 10 zuwa sama kuma za a sayar musu da kowace lita a kan N895.
Ta bayyana cewa karin farashin ya shafi duk kayan da ba a rika an dauka ba, kuma sabon farashin zai fara aiki ne daga karfe 5.30 na yamma, ranar Juma’a 17 ga Janairu, 2025.