Matatar Dangote ta rage farashin man fetur 

Matatar ta ce ta yi wannan ragi ne don nuna godiyarta kan yadda ‘yan Najeriya suka mara mata baya.

Matatar Dangote ta rage farashin man fetur 

Matatar Dangote ta yi wa ’yan kasuwa ragi game da farashin man fetur.

Babban Jami’in Matatar Dangote, Anthony Chiejina ne, ya sanar da hakan a ranar Lahadi, inda ya ce farashin ya ragu daga Naira 990 zuwa Naira 970 kan kowace lita.

“Wannan rangwame wata hanya ce ta nuna godiyarmu ga ‘yan Najeriya saboda goyon bayansu wajen ganin matatar ta zauna da ƙafarta,” in ji shi.

“Haka kuma, muna gode wa gwamnati bisa tallafinta wajen inganta kasuwancin cikin gida don amfanin kowa.”

Ya tabbatar da cewa matatar za ta ci gaba da samar da mai, mai inganci, tare da ƙara yawan samar da shi domin biyan buƙatun kowa.

“Babu wata fargabar ƙarancin mai,” ya ƙara da cewa.

Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na Gombe, ya rasu

Matatar Dangote ta rage farashin man fetur 

Na kusa zama ɗan ƙwaya a baya — Obasanjo

Cibiyar Athena ta horar da malamai 100 hanyoyin bunƙasa koyarwa a Katsina