Matatar Dangote ta rage farashin man fetur
Farashin mai ya faɗi a duniya bayan Trump ya yi hasashen kawo ƙarshen yakin Gabas ta Tsakiya nan ba da jimawa ba.
Matatar Dangote ta sanar da rage farashin man fetur daga naira 1,175 kan kowace lita zuwa naira 1,075, wato ragin naira 100 kenan.
Wata sanarwa da matatar ta wallafa a shafinta na X, ta ce matakin ya biyo bayan saukar farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya, kuma an yi hakan ne bisa sabon tsarin farashi da kamfanin ya fitar.
- Muna son kawar da barazanar da Iran ta daɗe tana yi mana — Isra’ila
- Pakistan ta yi wa sabon jagoran Iran ta’aziyyar mahaifinsa
Sanarwar ta kuma bayyana cewa matatar ta rage farashin man dizal zuwa naira 1,430 kan kowace lita, daga tsohon farashin naira 1,620.
A Talatar da ta gabata ce farashin mai ya faɗi a duniya bayan Shugaba Donald Trump ya yi hasashen kawo ƙarshen yakin Gabas ta Tsakiya nan ba da jimawa ba.
Man Fetur samfurin Brent ya faɗi da kusan kashi 10 zuwa ƙasa da dala 90 kowane ganga ɗaya a kasuwannin Asiya a ranar Talata, bayan da ya kai dala 119.50, farashi mafi tsada da aka taɓa gani tun tsakiyar 2022.