Matatar Dangote ta soma sayar da man dizel da na jirgin sama

Fara sayar da man ga ’yan kasuwa na cikin gida zai tilasta wa farashin man dizel sauka ƙasa da N1000 duk lita.

Matatar Dangote ta soma sayar da man dizel da na jirgin sama

Dangote da Otedola a matatar

Matatar mai ta Dangote ta fara sayar da albarkatun man fetur a ranar Talata, wani muhimmin mataki a yunkurin da ƙasar ke yi na samun dogaro da kai a fannin makamashi.

Daraktan rukunan kamfanonin Dangote Devakumar Edwin ya tabbatar da cewa sun fara sayar da man dizel da man jiragen sama a ƙasar.

Edwin ya shaida wa Reuters cewa “Muna da isasshen mai. Ana jigilar man ta ruwa da ƙasa. Jiragen ruwa na bin layi ɗaya bayan ɗaya don ɗiban dizel da man jiragen sama.

“Jiragen ruwa na ɗaukar lita miliyan 26, amma muna ƙoƙarin ganin an kawo jiragen da ke ɗaukar lita miliyan 37 don sauƙaƙa ayyukan.”

Ƙungiyar masu sayar da man ta amince kan sayar da kowacce litar dizel naira 1,225 bayan ƙulla yarjejeniya kan tsayar da farashi, in ji Abubakar Maigandi, Shugaban ƙungiyar Masu Sayar da Man Fetur Mai Zaman Kanta a Nijeriya.

Mambobin ƙungiyar na da gidajen mai kimanin 150,000 a faɗin Nijeriya, in ji Maigandi.

Kazalika, Manajan Darakta a Kamfanin kan harkokin Kuɗi, Bismarck Rewane, ya bayyana cewa fara sayar da man dizel ɗin daga matatar Dangote zai tilastawa farashin man dizal sauka ƙasa da Naira 1,000 kan kowace lita.

Matatar mai ta Dangote na so ta kawo ƙarshen dogaro ga man da ake shigowa da shi daga ƙasashen waje da Nijeriya ke yi.

Wannan babban matakin tsayawa da ƙafafu ga Nijeriya wajen biyan buƙatar makamashi da take da ita.

Mutumin da ya fi kowa kuɗi a Afirka, Aliko Dangote ne ya gina matatar man, mafi girma a nahiyar a gaɓar tekun Legas kan dala biliyan 20, kuma an kammala aikin bayan tsaiko na shekaru da dama da aka samu.

Matatar na iya tace gangar ɗanyen mai 650,000 kowace rana, kuma idan ta fara aiki ɗari bisa ɗari za ta zama mafi girma a Afirka da Turai.

Nijeriya ce kasar da ta kowace yawan jama’a a Afirka, kuma tana kan gaba a tsakanin ƙasashen da ke fitar da albarkatun mai, amma tana sayo mai daga waje saboda ba ta da matatu.