Matatar Dangote za ta fara rarraba man fetur ranar Lahadi

NNPCL ne zai rika sayen man daga Matatar Dangote sannan ya sayar wa ’yan kasuwa.

Matatar Dangote za ta fara rarraba man fetur ranar Lahadi

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta sanar da cewa a gobe Lahadi Matatar Dangote za ta soma rarraba tataccen man fetur a faɗin ƙasar.

Ministan Kudi, Wale Edun wanda Shugaban Hukumar Tattara Kudaden Shiga (FIRS), Dokta Zacch Adeji ne ya bayyana yayin wani taron manema labarai ranar Juma’a a Abuja.

Sanarwar ta ce Kamfanin Man Fetur na Nijeriya NNPCL ne zai dauki ragamar rarraba man da Matatar Dangote ke tacewa ga dillalan man kasar.

Matatar Dangote dai na tace danyen mai da ya kai yawan ganga dubu dari shida da hamsin a duk rana, lamarin da ya kawo karshen takaddamar da aka jima ana fuskanta kan batun rarraba man.

Ministan ya ce a gobe Lahadi NNPCL zai fara sayen man daga Matatar Dangote sannan ya rika sayar wa ’yan kasuwa a fadin kasar.

Al’ummar Nijeriya dai na fama da karancin man fetur a fadin kasar, a daidai lokacin da tsadarsa ke ci gaba da jefa jama’a cikin mawuyacin hali na kangin rayuwa.

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda

An saki matar Ekweremadu daga gidan yari a Birtaniya, ta dawo Najeriya