Matatar Dangote za ta samar da fetur lita 25m a kullum —NMDPRA
NNPCL ya kamala sa hannu kan yarjejeniyar sayar wa Matatar Dangote da danyen mai a kan farashin Naira
Hukumar Kasuwancin Man Fetur (NMDPRA) ta sanar cewa matatar man Dangote za ta rika samar da lita miliya 25 na man fetur a cikin gida a kullum a watan nan na Satumba.
Hakan na zuwa ne jim kadan bayan Matatar Dangote ta fara fitar da tataccen man fetur a ranar Talata.
NMDPRA ta sanar da haka ne bayan Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) ya kamala sa hannu kan yarjejeniyar saya wa katafariyar matatar da danyen mai a kan farashin Naira.
Ana iya tuna cewa Majalisar Zartarwa ta a amince NNPCL ya sayar wa matatar Dangote da danyen mai da Naira.
- Matatar Dangote ta fara fitar da tataccen man fetur
- Kuɗin man fetur ya ƙaru zuwa N1,200
- Zanga-zanga ta ɓarke kan wahalar man fetur
“Kuma tuni NNPCL ya kammala sanya hannu kan yarjejeniyar da Matatar Dangote wadda za ta rika samar da tataccen fetur lita miliyan 25 a cikin gida a watan Satumban 204, sannan ya karu zuwa lita miliyan 30 a watan Oktoba,” a cewar NMDPRA a lokacin sanya hannu kan yarjejeniyar.
A sanarwar da shugaban Matatar Dangote Refinery, Aliko Dangote, ya fitar, ya ce yarjejeniyar za ta rage dogaron Najeriya kan Dala da kashi 40%.
Dangote ya kuma bayyana godiya ga shugaban kasa kan wanna karamci.