Matatar Dangote za ta samar da rarar Dala biliyan 2.5 a fannin takin zamani

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ce  da zarar matatar mai ta Dangote ta fara aiki za ta taimaka wa Gwamnatin Tarayya wajen samun rarar Dala biliyan biyu da rabi  2.5 duk shekara ta hanyar samar da takin zamani na yuriya da sauran dangoginsa da za a rika fitar da su kasashen waje. […]

Matatar Dangote za ta samar da rarar Dala biliyan 2.5 a fannin takin zamani

Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ce  da zarar matatar mai ta Dangote ta fara aiki za ta taimaka wa Gwamnatin Tarayya wajen samun rarar Dala biliyan biyu da rabi  2.5 duk shekara ta hanyar samar da takin zamani na yuriya da sauran dangoginsa da za a rika fitar da su kasashen waje.

Baya ga nan matatar za ta taimaka wajen samar wa Najeriya kudaden musaya, kuma za ta samar da karin guraben aikin yi har dubu 70 da zarar ta fara aiki.

Fitaccen dan kasuwar yana wannan jawabi ne lokacin da Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Mista Godwin Emefiele, ya kai ziyarar ganin yadda aikin matatar ke tafiya a karshen makon jiya a Legas.

Dangote ya ce yana da kudirin rage rashin aikin yi da ke addabar kasar nan ta hanyar zuba jari a bangarorin tattalin arziki  daban-daban.

Baya ga samar da aikin yi ga ’yan Najeriya kamfanin zai kuma samar da kudaden musaya na kasashen waje da zarar Najeriya ta zama ta dogara da albarkatun man fetur da za a  daina shigowa da shi. Alhaji Aliko Dangote ya ce  “baya ga samar da aiki da muke yi, yanzu abin da muka sa a gaba shi ne mu samar da kudaden da suke zirarewa ta hanyar musaya da na waje da  zarar muka fara samar da albarkatun mai a cikin gida. Ba man fetur kadai za mu samar ba, duk wani abu da ake cirewa a jikin danyen mai za mu rika samar da shi  da kuma takin zamani. Za mu kasance daya daga cikin matatu mafiya girma da za su rika samar da kudaden waje,” inji shi.

Dangote ya ce a cikin watan Mayun bana bangaren daya da zai samar da takin zamani na yuriya zai fara aiki a yankin Ibeju Lekki a Jihar Legas.

A cewar Dangote bangaren da zai samar da takin zamani zai sa Najeriya ta zama ta daya a yankin Afirka Kudu da Sahara wajen fitar da takin zamani zuwa kasashen waje kuma kamfanin zai zama jagaba wajen samar da sindaran da ake leda da robobi da su wanda hakan zai taimaka wajen samar da Dala biliyan biyu da rabi duk shekara.

Ya ce “Nan bada jimawa ba Najeriya za ta zama ta daya a yankin Afirka Kudu da Sahara wajen samar da takin zamani na yuriya a karon farko cikin tarihi, ba wai za mu fitar da shi ba ne kadai a’a za mu fitar da babbar harka ce zuwa waje.

“Ina tsammani ya kamata mu gode wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari saboda irin tsare-tsaren da ya fito da su na tattalin arziki, kuma muna gode wa Gwamnan Babban Bankin Najeriya  wajen rage kudaden ruwa ga masu niyyar samar da gagarumin aiki irin wannan,” inji shi.

A nasa bangaren Gwamnan Babban Bankin ya ce ya gamsu da irin  yadda aiki ke gudana a wannan wuri kamar yadda aka tsara kuma ya gamsu da irin kayan aikin da ya gani a wannan wuri.

Ya ce “Dalilin da ya sa na ziyarci wannan wuri shi ne don na gane wa ido na abin da ke wakana a wannan aiki. A halin yanzu tattalin arziki ya shiga wani yanayi da ya zama wajibi mu mai da hankali ga wasu bangarori  ba wai dogaro a kan man fetur ba, tun da muna da wadatar albarkatun kasa.”

Emefiele, ya ce sashin samar da taki zai dakatar da shigo da takin zamani zuwa Najeriya, sannan  kashi 25 cikin 100 na takin za a rika amfani da shi ne a cikin gida domin habaka harkar noma a Najeriya.

A cewarsa kamfanin zai samar da  akalla Dala miliyan 750 wajen fitar da taki zuwa waje duk shekara.

“Matatar tana da karfin tace gangar danyen mai dubu 650, idan ta fara aiki baya ga samar da man da za a yi amfani da shi a cikin gida za ta kuma maida Najeriya jagaba wajen fitar da albarkatun man fetur zuwa waje. Najeriya tana da damar da za ta samar da isasshen man da ake bukata a Nahiyar Afirka baki daya kuma hakan zai sa man ya zama mai saukin saye a nahiyar. Wannan gagarumin aikin ya zo a lokacin da ya dace da Najeriya za ta yanke farashin mai a cikin gida  da kuma waje ta hanyar zama mai sauki ciki da wajen Nahiyar Afirka.”

“Ya kamata mu rika karfafa wa ’yan Najeriya gwiwa wajen sanya jari don kafa irin wadannan masana’antu, kuma za mu ci gaba da fada musu cewa su tashi su tsaya da kafafunsu su taimaki kasarsu,” inji Gwamnan Babban Bankin.