‘Matatar man Ɗangote za ta fara aiki a watan Nuwamba’
A baya dai an tsara matatar za ta fara aiki a watan Agusta
Matatar man attajirin nan na Najeriya, Aliko Dangote za ta fara aiki a watan Nuwamba mai zuwa, in ji Babban Daraktan rukunin kamfanonin Dangote, Devakumar Edwin.
A cewarsa, matatar za ta fara da tace man fetur ranar 30 ga watan Nuwamba, sai kuma man dizal da na jirgi a watan Oktoba mai zuwa.
Babban Daraktan ya ce za su karbi jirgin ruwa dauke da danyen mai na farko nan da mako biyu masu zuwa, sannan zai fara samar da har ganga 370,000 na dizal da man jirgi ya zuwa watan Oktoban 2023.
Kazalika, ya ce sannu a hankali matatar za ta ci gaba da kara man fetur din da take tacewa har sai ya kai ganga dubu 650 a kullum nan da ranar 30 ga watan Nuwamban.
Ya ce, “Yanzu haka a shirye matatar mu take ta fara tace man da zarar jirgin ruwa na farko ya iso.”
Dangane da dalilin da ya sa matatar ta dage fara aiki kamar yadda ta tsara a watan Agusta, Devakumar, ya ce hakan ta faru ne sakamakon Kamfanin Mai na Najeriya (NNPCL) ya bayar da man da aka shirya ware musu tun da farko ga wani kamfanin.
Sai dai ya ce jinkirin na dan lokaci ne, kuma matatar za ta fara tace iya man da ake hakowa daga Najeriya zalla nan da watan na Nuwamba.
Sai dai ya ce matatar za ta rika sayen danyen ne da Dalar Amurka ba wai da Naira ba.
Devakumar ya kuma ce matatar za ta rika sarrafa man da za a rika amfani da shi a akasarin kasashen Afirka da Gabas ta Tsakiya da ma wani bangare na Amurka.