Matatar man Dangote za ta fara aiki nan da mako 2

Buhari zai kaddamar da matatar mako guda kafin saukarsa daga mulki

Matatar man Dangote za ta fara aiki nan da mako 2

Matatar Mai ta Dangote

Nan da mako biyu masu zuwa katafariyar matatar mai ta Dangote mai karfin samar da ganga dubu 650 na tataccen mai a kullum za ta fara aiki.

Babban Jami’in Hulda da Jama’a na Rukunin Masana’antun Dangote, Anthony Chiejina, ya sanar a ranar Lahadi cewa za a kaddamar da sabuwar matatar ne ranar 22 ga watan Mayu da muke ciki.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne zai a kaddamar da matatar man a Legas, mako guda kafin saukarsa daga mulki.

Gwamnatin Tarayya na sa ran fara aikin sabuwar matatar, wadda kamfanin mai na kasa (NNPCL) ke da hannun jari a ciki, zai taimaka wajen magance matsalar mai da ake fama da ita a Najeriya.

Sabuwar masana’antar ta Dangote za ta kuma rika samar sauran dangogin man fetur daga danyen mai da take tacewa.

Matatar, wadda aka gina a kan kudi Dala biliyan, ita ce mafi girma a daukacin nahiyar Afirka, kuma ta zarce da dama daga cikin manyan masan’antun mai na duniya.