Matatar man fetur ta Dangote ta soma aiki
Idan matatar ta fara aiki ɗari bisa ɗari za ta iya tace duk man fetur da ake buƙata a Najeriya.
Rahotonni sun bayyana cewa matatar mai ta Dangote wadda aka ƙaddamar tun a bara ta fara aiki a wannan Juma’ar.
Babbar matatar da ke birnin Legas ta fara aikin ne bayan kammala ta tare da ƙaddamar da ita a matsayin matatar mai mafi girma a nahiyar Afirka.
- Tinubu ya naɗa Ali Nuhu Shugaban Hukumar Fina-Finai ta Kasa
- Tinubu ya dakatar da shirye-shiryen yaƙi da talauci na hukumar NSIPA
Matatar ta fara aikin ne bayan tara kimanin ganga miliyan shida na ɗanyen man fetur a wannan makon.
A watan Disambar bara ne matatar ta tabbatar da cewa ta fara karɓar ɗanyen man fetur wanda za ta fara tacewa domin samar da man fetur da sauran dangoginsa na abubuwan amfani.
A watan Nuwamba ne kamfanin mai na NNPC ya sanya hannu kan wata yarjejeniya ta samar da ɗanyen man fetur ga matatar.
Wannan dai wani lokaci ne da aka daɗe ana jira a ƙasar ta Najeriya, ganin cewa ana sa ran matatar za ta sauya harkokin man fetur a ƙasar.
Duk da cewa Najeriya ce kan gaba wajen fitar da ɗanyen mai a Afirka, amma ba ta iya tace shi domin samar da man fetur domin amfani a ƙasar, wadda ita ce kan gaba wajen yawan jama’a da ƙarfin tattalin arziƙi a Afirka.
A cikin wata sanarwar da ta fito daga matatar tun a bara, ta ambato shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote na cewa “wannan mataki ne mai muhimmanci.”
Tun a wancan lokaci an bayyana cewa idan matatar ta fara aiki ɗari bisa ɗari za ta iya tace duk man fetur da ake buƙata a Najeriya har ma a samu rara da za a fitar zuwa wasu ƙasashe a kullum.
An tsara ta yadda za ta iya sarrafa nau’uka daban-daban na ɗanyen mai daga ƙasashen Afirka da na ƙasashen Gabas ta Tsakiya da yankin Amurka.
Matatar tana da manyan tankuna 177 waɗanda za su iya ɗaukar mai da yawansa ya kai lita biliyan 4.742.
A watan Mayun 2023 ne tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da sabuwar matatar man mallakin mutum mafi arziƙi a Afirka, Aliko Ɗangote.
An ƙaddamar da matatar ce kimanin shekaru 67 bayan da Najeriya ta fara samar da ɗanyen man fetur a 1957.
Tun bayan da aikin samar da matatar man ya kankama al’ummar Najeriya sun zaku su ga fara aikinta, kasancewar suna kyautata zaton cewa za ta kawo sauki ga samuwar man fetur a fadin kasar.