Matatun man fetur 4 za su fara aiki a Najeriya a badi — Minista
Burinmu shi ne nan da ’yan shekaru ƙalilan, Najeriya ta daina shigo da man fetur cikin ƙasar.
Gwamnatin Tarayya ta ce tana sa rai matatun man fetur ɗin ƙasar guda huɗu za su koma aiki nan da ƙarshen shekara mai zuwa.
Sabon ƙaramin ministan man fetur na Najeriya, Heineken Lokpobiri ne ya bayyana hakan ranar Juma’a kamar yadda BBC ya ruwaito.
- Kwankwaso ya halarci addu’ar da aka shirya kan shirin ƙwace zaɓen Abba
- Nijar ta koro jakadan Najeriya
Ya ce matakin zai fara tabbata ne da matatar man fetur ta Fatakwal wadda ake kyautata tsammanin za ta fara aiki a farkon watan Disamban bana.
A baya dai, gwamnatin Najeriya ta ce matatar mai ta Fatakwal za ta fara tace ɗanyen man fetur a ƙarshen 2022, kuma ministocin man fetur da kamfanin NNPPC sun sanar da shirye-shiryen da ba su yi nasara ba, na sake farfaɗowa da bunƙasa matatun man fetur a ƙasar.
A farkon wannan mako ne, Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da Heineken Lokpobiri a matsayin ƙaramin ministan man fetur, inda a yau Juma’a ya je rangadi na aikin gyare-gyaren da ake ci gaba da yi a matatar man fetur ta Fatakwal mai sashe biyu da ke iya tace ganga 210,000.
“Daga abin da na gani a nan yau, zuwa ƙarshen shekara, ba shakka matatar mai ta Fatakwal za ta fara aiki,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa sauran matatun mai biyu na Warri da Kaduna za su fara tace man fetur ko dai a cikin wata uku na farko da kuma a ƙarshen shekara ta 2024.
Lokpobiri ya ce “burinmu shi ne tabbatar da ganin nan da ’yan shekaru ƙalilan, Najeriya za ta daina shigo da man fetur cikin ƙasar.”
Najeriya, ita ce ƙasar da ta fi haƙo man fetur a Afirka, amma kusan duk tataccen man fetur ɗinta tana shigo da shi ne daga ƙetare.
Tsawon shekaru da rufe matatun man fetur ɗin guda huɗu mallakar gwamnati, inda gaba ɗayansu suna iya tace ɗanyen mai ganga 4450,000 a kullum.