Matawalle na da ’yancin neman a binciki Fadar Shugaban Kasa —Gwamnati 

Gwamna Matawalle ya bukaci EFCC, ta ya daina takura wa gwamnoni da bincike, ta waiwaya kan fadar Shugaban kasa da ministoci masu barin gado

Matawalle na da ’yancin neman a binciki Fadar Shugaban Kasa —Gwamnati 

Lai Mohammed

Gwamnatin Tarayya ta ce Gwamna Bello Matawalle na Jihar Zamfara yana da ’yancin fadin albarkacin bakinsa na bukatar Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta fadada bincike kan jami’an da ke cin rashawa zuwa Fadar Shugaban Kasa da kuma ministoci masu barin gado.

Gwamna Matawalle a cikin wata sanarwa da ya fitar ya bukaci Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa, da ya daina takura wa gwamnoni da bincike, ya waiwaya kan fadar Shugaban kasa da ’yan Majalisar Zartarwa ta Tarayya.

Ya bukaci shugaban na EFCC da ya tabbatar da cewa binciken hukumar ya zama cikakke ba tare da nuna wariya ba.

Ya ce, “Ina bukatar shugaban EFCC ya yi irin wannan gayyata ga jami’an Fadar Shugaban Kasa da kuma mambobin majalisar zartarwa ta tarayya, wadda ita ce mafi girman matakin gwamnati a kasar nan.”

Sai dai gwamnatin tarayya a martaninta ta bakin Ministan Yada Labarai da Raya Al’adu, Lai Mohammed, ta ce gwamnan ya bayyana ra’ayinsa ne, na kashin kansa.

Da aka nemi jin ta bakinsa, Lai Mohammed ya ce, “Gwamna na da ’yancin bayar da shawarwari, ra’ayinsa ke nan.”