Matawallen ne gwarzon kabilun Jihar Zamfara
Tun daga shekarar 1999 dundumin siyasa ya baibaye mutanen Jihar Zamfara, har ta kai ga al’umma ta rasa yadda za ta kare ra’ayinta. Bisa la’akari da wannan ne ta sanya Hadaddiyar kungiyar kabilun da ke fadin jihar ta gwammace ta goyi bayan jam’iyyar PDP. Domin mun la’akari da nasarorin da kowane mai mulki ya samu […]
Tun daga shekarar 1999 dundumin siyasa ya baibaye mutanen Jihar Zamfara, har ta kai ga al’umma ta rasa yadda za ta kare ra’ayinta. Bisa la’akari da wannan ne ta sanya Hadaddiyar kungiyar kabilun da ke fadin jihar ta gwammace ta goyi bayan jam’iyyar PDP. Domin mun la’akari da nasarorin da kowane mai mulki ya samu tun daga kan Alhaji Ahmad Sani Yariman Bakura, wanda ya fara zama gwamnan jihar mai cikakken iko bayan da dimokuradiyya ta kama kasa; kuma ya shafe shekaru takwas, tare da samun nasarori wajen samar da kayan more jin dadin rayuwa da bayar da rancen sayen gidaje ga ma’aiaktan gwmanati, da gina gajerun hanyoyi, sannan ya tabbatar da kafuwar Shari’a a Jihar Zamfara.
Bisa la’akari da kima da darajar kowane dan takarar Gwamna a Jihar Zamfara, kungiyar hadin gwiwar kabilun da ke zaune a fadin jihar tabbas za su kasance masu biyayya ga jaj’iyyar PDP,musamman ma ganin cewa gwarzonmu Matawallen Maradun, Dokta Bello Mohammed, wanda ya kasance kai kadai gayya. Domin a lokacin da tsohon Gwmanan Jihar Zamfara, Alhaji Mamuda Aliyu Shinkafi ya fadi zabe a shekarar 2011, Dokta Bello ne kawai ya rika daukae dawainiyar jam’iyya data al’umma. Kuma kujerar da wannan gwamnan na yanzu ke kai, ai tasa ce, aka kwace masa a jam’iyyar ANPP.Duk da irin yankan baya da zagon kasa da aka yi masa, mu dai muna da tabbaci cewa ‘sara da sassaka ba sa hana gamji toho.’
Dokta Muhammad Bello,Matawallen Maradun yana da kyakkyawar mu’amala da mutanen Jihar Zamfara, kuma ya taba bai wa talakawaklayan tallafin sana’a a mazabarsa. Mutum ne mai fara’a da shimfidar fuska, gakuma kwarjini. Wannan gwarzo na al’umma, shugaba ne wanda ke jan kowa da kowa a jika don warware matsalolin da suka addabi al’umma, sannan a gudu tare, a tsira tare.
Ganin irin namijin kokarin Matawallen Maradun ta sanya mu dage kan cewa lallai sai ya yi takara a jam’iyyar PDP, kuma za mu hada kai da duk masu son ci gaban wannan jiha, ’yan asalin jihar ne, ko kuwa mazauna, su zo mu tafi tare, don ganin mun samar wa mutanen Zamfara shugabanci nagari.
Tabbas kur’ani da littafin Baibul na dauke hukunce-hukuncen da Allah Ya saukar wa mutane, kuma yanke hukunci yana nan a cikin abin da Annabawa suka zo mana da shi. Don haka mutanen da suka hada da . Alhaji Abubakar Abugi da Kanayo Okoli a matsayin shugabanninmu a wannan fafutika, sai kuma sakatarenmu Alhaji Taliat Tijani da Shugabar Mata, Madam Rita James, duk mun amanna da cewa, Matawalle shi ne zai tabbatar da adalci ga kabilun Jihar Zamfara. Saboda haka muke kira ga masu son ci gaba a wannan jiha ta mu, kada su yarda a cika da baza kalaman batanci ga shugabanni, musamman wadanda manufarsu su kyautata rayuwar al’umma. Idan har da gaske muke a wannan fafutika, to mu dage wajen ganin mun samu nasara, kuma Allah Ya taimake mu, mu ga ranar da Matawalle zai dare bisa kujerar Gwamnan Jihar Zamfara a shekarar 2015.
Mun kasance masoyan Dokta Bello Mohammed ne don ya warware mana matsalolin da suka addabi ilimi, ya fadakar da al’umma hanyoyin da suka dace su bi don ganin an tafi da su a cikin harkokin siyasar kasar nan. Bisa wannan kuduri ba ja da baya. Muna ganin Jam’iyyar PDP da Dokta Bello Mohammed sun yunkuro don kyautata rayuwar al’umma. Sai mu hada karfi don cimma manufar al’umma.
Babban farin cikinmu shi ne, za mu so kafafen yada labarai su yi awo a sikeli, kan kima da darajar kowane dan takara, sannan su tankade, su rairaye, su fito wa mutanen Jihar Zamfara mutmin da ya cancanta, ta yadda za a gano yadda Matawalle ya shiga gaban maza. Abin lura ga masu neman mulki, shi ne kokarinsu da tasirinsu wajen inganta rayuwar al’umma, a harkokin zamantakewa da tattalin arziki da siyasa. Don haka wanda duk ba shi da wani kuduri na neman hadin kan al’umma wajen warware matsalolinsu, to ba shi da wata nagarta. Saboda haka sai mu hankalta, tun lokaci bai kure ba.
Alhaji Abugi ya rubuto makalarsa ne daga Jihar Zamfara.