Matsa mini aka yi na zama Shugaban kasa – Gowon
Tsohon shugaban mulkin soja Janar Yakubu Gowon ya ce bai nemi zama Shugaban kasa ba lokacin da ya dawo daga kwas a 1966, matasan hafsoshin soja ne suka matsa ya jagoranci kasar nan yana dan shekara 32. Janar Yakubu Gowon ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai kan cikarsa shekara 80 […]
Tsohon shugaban mulkin soja Janar Yakubu Gowon ya ce bai nemi zama Shugaban kasa ba lokacin da ya dawo daga kwas a 1966, matasan hafsoshin soja ne suka matsa ya jagoranci kasar nan yana dan shekara 32.
Janar Yakubu Gowon ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai kan cikarsa shekara 80 a duniya, inda ya ce bai ma son zama Shugaban kasa, amma son da yake wa kasarsa da yakinin da ’yan uwansa sojoji suke da ita a kansa ya karfafa masa gwiwa ya canja ra’ayinsa, kuma ya ce wannan shawara tana daya daga cikin mafiya girman kalubale da ya fuskanta a rayuwarsa.
Game da yadda aka yi ya zama Shugaban kasa, Janar Gowon ya ce, “Idan za ku tuna, an samu awa 48 babu Shugaban kasa, kuma manyan sakatarori suna bukatar wanda zai jagoranci kasar nan, inda za su rika karbar umarni daga gare shi don gudanar da ayyukansu.”
Ya ce a lokacin ne matasan hafsoshin soja suka yanke shawarar cewa suna bukatarsa ya zama Shugaban kasa. “Matasan hafsoshin soja ne suka dora ni a kan kujerar, inda manyan hafsoshin soja suka amince da hakan.”
Da yake waiwaye kan Yakin Basasar kasar nan na wata 30 da aka fara a 1967, Janar Gowon ya bayyana shi da wani babban kalubale da ya fuskanta domin tabbatar da Najeriya a matsayin kasa daya.
Ya ce sun yi iyakar kokarinsu domin su dakatar da tashin hankali a Arewa tare da dawo da zaman lafiya a kasar a samu zaman lumana da ci gaba, amma sai Yakin Basasa ya barke, lokacin da Ojukwu ya ayyana ’yancin kasar Biyafara.
Janar Gowon ya ce daga farko ya so yin amfani da ’yan sanda wajen dawo da bin doka a yankin Gabas. “Kun san Yakin Basasa ya faru ne sakamakon ayyana ballewa da Ojukwu ya yi. Da bai ayyana ballewa ba, ya ce yankinsa ya fice daga Najeriya ba, gaskiya ba za a samu Yakin Basasa ba. Da an yi amfani da ’yan sanda waje dawo da doka da oda, wannan shi ne abin da na yi kokarin yi kafin Yakin Basasa.”
Ya ce Yakin Basasa ba cikakken yaki ne da abokan gaba ba, a’a yaki ne da wadanda suka adawa da hadin kan Najeriya. Ya ce wannan ya sa aka gudanar da yakin bisa taka-tsantsa don kauce wa muguwar barna da cutarwa.
Janar Gowon y ace kawo karshen Yakin Basasar ya zame masa daya daga cikin ranaku mafiya farin ciki, musamman da ya zamo ba a koma yakin sari-ka-noke ba.