Matsa wa Shata na yi ya yi mini waka – Indon Musawa

“Mace mai kyau mai kyan diri da kyan fara’a Indon Musawa. Daga kwance kamar kumsa ga dadin fadi kamar ba sim lallan hakuri.” -Dokta Mamman Shata a wakarsa ta Indon Musawa Indon Musawa na cikin matan da marigayi Alhaji Mamman Shata Katsina ya yi wa waka lokacin rayuwarsa, kuma Aminiya ta yi hira da ita […]

Matsa wa Shata na yi ya yi mini waka – Indon Musawa

“Mace mai kyau mai kyan diri da kyan fara’a Indon Musawa.

Daga kwance kamar kumsa ga dadin fadi kamar ba sim lallan hakuri.”

-Dokta Mamman Shata a wakarsa ta Indon Musawa

Indon Musawa na cikin matan da marigayi Alhaji Mamman Shata Katsina ya yi wa waka lokacin rayuwarsa, kuma Aminiya ta yi hira da ita a gidan da take zaune a Unguwar Fagge cikin birnin Kano, inda ta yi bayanin dalilin ya sanya Shata ya yi mata waka, ta ce ba ta ba Shata ko kwabo ba, illa iyaka kasancewarsu makwabta, takan je fili idan yana waka ta ce atafau sai ya yi mata waka:

Abubakar AbdurRahaman Dodo a Kano

Aminiya: Ko za ki ba mu takaitaccen tarihinki?
Indon Musawa: Ban san shekaruna ba, saboda ba na iya ganewa, tun da abubuwa sun same ni yanzu, girma ya zo, duk abubuwa da yawa na manta. Yanzu haka wani a cikin gidan ma na manta sunansa. Kuma asalina ba a Musawa aka haife ni ba. Garinmu Sabon Garin Gangara a yankin Musawan ne dan kauyen yake. Na dai wuce shekara 60, amma wannan yaron ya rike (jikanta, wanda ya ce ta kai 93).
Aminiya: Lokacin da kike yarinya ko za ki iya tuna wanda yake sarauta a Katsina?
Indon Musawa: Sarki Dikko ne.
Aminiya: Yaya aka yi kuka hadu da Shata har ya yi miki waka?
Indon Musawa: Rigima ce ta sa ya yi mini waka. Domin Alhaji Mamman Shata makwabcinmu ne a Musawa. Mun taso gaba daya. Wurin rigima ce. Idan yana tsakiyar yin waka, sai in je in hana, in ce, ni ma sai an yi mini. Kuma ni ba kudi nake ba shi ba, ni kanwarsa ce. Sai in rikice in ce sai an yi mini waka. Sai ya zage ni kuma in ce ko ka zage ni, ka zagi banza sakarai, sai ka yi mini waka. Shi ne fa sai ya yi wakar. Idan kuma ya yi wakar sai hankalina ya dawo jikina. Sai a daidaita.
Aminiya: Me kike so a cikin wakar da Shata ya rera miki?
Indon Musawa: Ina jin dadin da yake cewa: “Mace mai kyau Indon Musawa, ga kyan diri!”
Aminiya: Wacce irin daukaka wakar Shata ta jawo miki?
Indon Musawa: Wakar Shata ta jawo mini daukaka da yawa. Ta sanya an san ni a duniya. Indon Musawa din nan.
Aminiya: Ko mutane na zuwa ganin ki saboda wakar Shata?
Indon Musawa: Da suna zuwa, amma da dadewa.
Aminiya: Me ya kawo ki Kano?
Indon Musawa: Yawo ya kawo ni Kano, kuma tun da na zo ban taba koma wa gida na zauna ba, sai dai haka in je in kwana biyu in komo. Kai har ’yan gida sukan biyo ni.
Aminiya: Wacce irin rashin lafiya ke damunki yanzu?
Indon Musawa: Numfashina yana daukewa, ya dawo ga girma. Wani lokacin ba na iya magana. Yanzu ka ga ba ni iya fitowa waje, kusan kullum ina daki.
Aminiya: A dakinki na ga hotunan ’yan siyasa, ga rigarki ta ’yan siyasa, shin wacce siyasa kika yi?
Indon Musawa: Na yi NEPU, sai kuma ta Kwankwaso da Ganduje.
Aminiya: An ce kin yi aikin shara a lokacin Malam Shekarau, har yanzu kin ci gaba da yi ne?
Indon Musawa: Eh, na yi shara lokacin Shekarau. Wallahi ba gaira ba dalili aka cire mu. Muna shararmu aka cire mu a zamanin wannan Gwamna na yanzu wato Kwankwaso.