‘Matsafa na bin makabartu su hako gawarwakin ’yan uwanmu’
Matsafa na bin dare su hako gawarwaki domin yin surkulle
Mazauna unguwar Wurakum da ke Karamar Hukumar Bassa ta Jihar Filato sun koka bisa yadda matsafa suka addabe su da hako gawarwaki daga kaburbura a yankin.
Shugaban al’ummar Wurakum, Aminu Ahmad Babayo, ya ce matsafa kan bi sabbin kaburbura suna hako gawarwaki a cikin dare domin biyan bukatun kansu.
- NAJERIYA A YAU: Shekara 23 Da Mulkin Dimokuradiyya: Ina Aka Kwana?
- ’Yan bindiga sun yi awon gaba da limaman coci 3 a Kogi
Ya ce, “Wani lokaci idan suka hako gawarwakin sukan cire sassan jikin gawar, wani lokaci kuma kabarin suke tonawa su sanya wani abu a ciki, watakila saboda tsafi.”
Ya bayyana cewa a lokuta da dama idan aka binne gawa, matsafan suka bin dare a ranar ko washegari su haka bakarin domin yin surkullensu.
Da yake bayyana damuwa kan yadda ya ce neman abin duniya ya rufe wa mutane ido, Aminu Ahmad Babayo, ya yi kira ga jama’a da su ji tsoron Allah a duk abin da suke yi, domin akwai ranar da kowa zai tsaya a gaban Allah a yi mishi hisabi.