Matsafa sun kashe tsoho sun kwashe sassan jikinsa
Da sanyin safiyar Alhamis ta makon jiya ne wasu ’yan uwan dattijo Pa Raheem Oyeniyi, dan shekara 85 suka kwankwasa kofar shiga cikin gidansa domin sanin dalilin da ya hana shi zuwa masallaci don Sallar Asuba ta wannan rana kamar yadda ya saba, amma suka ji shiru babu amsa. Sai suka yanke shawarar kalla kofar, […]
Da sanyin safiyar Alhamis ta makon jiya ne wasu ’yan uwan dattijo Pa Raheem Oyeniyi, dan shekara 85 suka kwankwasa kofar shiga cikin gidansa domin sanin dalilin da ya hana shi zuwa masallaci don Sallar Asuba ta wannan rana kamar yadda ya saba, amma suka ji shiru babu amsa. Sai suka yanke shawarar kalla kofar, inda suka shiga cikin gidan suka tarar da gawarsa, an yanke kokon kai da kayan cikinsa da mazakutarsa, an yi awon gaba da su; aka bar gangar jiki yashe cikin jini a cikin gidan nasa da ke unguwar Oke-Apo cikin garin Oyo.
A lokacin da wakilinmu ya ziyarci gidan marigayin a garin Oyo, ya tarar da kofar gidan a kulle kuma mutanen da ke zaune a kofar gidan da ake kyautata zaton ’yan uwan marigayin ne sun ki cewa komai dangane da wannan al’amari kuma sun ki yarda a dauki hotonsu. Shi kuwa mai unguwar Oke-Apo, Baale (Cif) Waheed Oyeniyi, cewa ya yi: “Ba za mu iya cewa komai a kan wannan al’amari ba, domin juyayin kisan gillar da aka yi wa wannan dattijo, jagora a cikin al’umma ta ishe mu. Kuma a matsayin mai unguwa a karkashin mai martaba Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Olayiwola Adeyemi, bai kamata wata magana ta fito daga bakina ba tare da izininsa ba.”
Amma wata majiya da aka sakaya sunanta ta shaida wa wakilinmu cewa: “Muna zargin daya daga cikin ’ya’yan kannen marigayin da hannu wajen aikata wannan danyen aiki domin ya ziyarci gidan Dattijo Pa Oyeneyi da yammacin ranar Laraba, ya yi tsaye a kofar gidan. Wannan matashi ya yi kaurin suna wajen zukar hayakin tabar wiwi da ake ganin alamar ta juye masa kwakwalwa. Ba a sake yin ido biyu da shi ba tun daga lokacin da wannan al’amari ya auku.” Inji majiyar.
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Oyo, Mista Leye Oyebade, ya ce ya bayar da umarnin hanzarta mika wannan matsala daga ofishin ’yan sanda na garin Oyo zuwa sashen binciken manyan laifuka na ’yan sandan ciki (CID) da ke Iyaganku a Ibadan, inda za a ci gaba da binciken gano dukkan masu hannu wajen kisan wannan dattijo domin a mika su ga kotu da za ta yanke masu hukumci daidai da irin laifin da suka aikata.