Matsafa sun kwace bindiga daga hannun ’yan sanda a Bayelsa
Wasu ’yan bindiga da ake kyautata zaton matsafa ne sun yi wa wani ayarin ’yan sanda kwanton bauna a kan hanyar Kolo zuwa Ogbia da ke Karamar Hukumar Ogbia ta Jihar Bayelsa. Rahotanni sun ce a sakamakon harin, wani jami’in dan sanda mai mukamin Insfekta ya ji mummunan rauni, sannan an yi awon gaba da […]
Wasu ’yan bindiga da ake kyautata zaton matsafa ne sun yi wa wani ayarin ’yan sanda kwanton bauna a kan hanyar Kolo zuwa Ogbia da ke Karamar Hukumar Ogbia ta Jihar Bayelsa.
Rahotanni sun ce a sakamakon harin, wani jami’in dan sanda mai mukamin Insfekta ya ji mummunan rauni, sannan an yi awon gaba da bindigarsa.
- An kama uba ya kai ’yan daba su doki malamin ’yarsa a makaranta
- An kashe fararen hula 1,153 da soja 105 a wata 3 a Najeriya
A cewar wata majiya daga yankin na Kolo, lamarin ya faru ne wasu ’yan mintuna kafin karfe 12:00 na daren ranar Litinin.
Ya ce a lokacin da mazauna yankin suka ji karar harbe-harbe, sun yi zaton tsagerun Neja Delta ne suka kai musu hari.
Duk da ana rade-radin cewa wani jami’in dan sanda ya rasa ransa, amma Kakakin ’yan sandan Jihar, SP Asinim Butswat ya ce jami’in rauni kawai ya samu.
Kakakin ya ce yanzu haka suna ci gaba da bincike a kan lamarin.
Ya ce, “Wasu mahara da muke kyautata zaton matsafa ne sun kai wa jami’anmu da ke binciken ababen hawa a kan hanyar Kolo zuwa Ogbia hari ranar 11 ga watan Oktoban 2021, da misalin karfe 10:45 na dare.
“A sakamakon haka, jami’in dan sanda daya ya ji mummunan rauni kuma an kwace bindigarsa. Muna ci gaba da bincike don ganin mun gano bata-garin da kuma kama kwato bindigar,” inji Kakakin.