Matsafa sun mika wa sabon Ooni hular mulki
Matsafan garin Ile-Ife su 201 ne suka warwatsu a garin a sa’ilin da suka bai wa sabon Ooni na Ife Oba, Adeyeye Enitan Ogunwusi hular mulki a daidai wurin da Oduduwa, wanda aka hakikance cewa shi ne asalin zuri’ar Yarabawa, ya sanya tasa hular mulkin. Sabon Ooni ya karbi hular sarautar ta Aare daga wajen […]
Matsafan garin Ile-Ife su 201 ne suka warwatsu a garin a sa’ilin da suka bai wa sabon Ooni na Ife Oba, Adeyeye Enitan Ogunwusi hular mulki a daidai wurin da Oduduwa, wanda aka hakikance cewa shi ne asalin zuri’ar Yarabawa, ya sanya tasa hular mulkin.
Sabon Ooni ya karbi hular sarautar ta Aare daga wajen Olajudo na lardin Edo a ranar Litinin din da ta gabata. A cewar wasu matsafa mabiya addinin gargajiya, sabon Ooni ba shi da ikon sanya hular mulkin a yanzu, domin ana sanya ta ne sau daya tilo a shekara, a lokacin bukukuwan Olojo; wanda za a yi nan ba da jimawa ba. Sun kuma kara da cewa hular mulkin ta Aare, wacce ake kira ‘Ade Oduduwa’ ta bar Ile-Ife ne tun lokacin da tsohon Ooni Oba Okunade Sijuade ya mutu.
A daidai lokacin da sabon Ooni ya shiga fadarsa ce aka yanka rago, aka yayyyafa jininsa a jikin daben harabar wajen, baya ga haka matsafan sun yi yanke-yanke inda suka umurci makada su sanar da bayyanar sabon Ooni na Ife Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi.
Sarkin Hausawan Ile-Ife, Alhaji Muhmuda Lawal Madagali ya shaida wa Aminiya cewa a yanzu sabon Oonin ya shiga fadarsa bayan ya shafe kwanaki 21 a gidan tsafi, sai dai a wannan karon sabon Oonin ya zauna cikin gidan tsafin ne a zamanance; domin yana shiga ne karfe 3 na rana ya fito 8 na dare a maimakon ya tare gaba daya a gidan.
A yanzu dai abin da ya rage shi ne bukin bai wa sabon Oonin sandar sarauta, wanda za a yi a ranar 7 ga watan gobe.