Matsafa sun sare kan mahaukaci a Jihar Nasarawa
Wasu da ba a san ko su wane ne ba da ake zargin matsafa ne sun sare kan wani mahaukaci sun tafi da kan. Lamarin ya faru ne a Unguwar Madauci da ke karamar Hukumar Doma a Jihar Nasarawa. Mahaukacin mai kimanin shekara 35 mai suna Isma’ula Akuki ya dade yana fama da tabin hankali […]
Wasu da ba a san ko su wane ne ba da ake zargin matsafa ne sun sare kan wani mahaukaci sun tafi da kan. Lamarin ya faru ne a Unguwar Madauci da ke karamar Hukumar Doma a Jihar Nasarawa.
Mahaukacin mai kimanin shekara 35 mai suna Isma’ula Akuki ya dade yana fama da tabin hankali kafin miyagun matsafan su sare masa kai da daddare.
Da ya ke jajanta wa iyalan marigayin Shugaban karamar Hukumar Doma, Mista Henry Omaku ya bayyana kisan gillar da aka yi wa mahaukacin da rashin imani da rashin tausayi, inda ya ce ba shakka dole ne wadanda suka aikata wannan danyen aiki su fuskanci hukuncin Allah.
Ya kara da cewa duk da yake wanda lamarin ya shafa mai tabin hankali ne amma ba ya kula kowa balle ya zagi wani. Daga nan sai ya yi alkawarin hada kai da jami’an tsaro a yankin don tabbatar wadanda ke aikata miyagun ayyuka a yankin sun shiga hannu.
Ya shawarci al’ummar yankin su rika kula da al’amuran tsaro a koyaushe don kare kansu da iyalansu baki daya.
Wasu daga cikin iyalan marigayin Jibrin Ukyawu da Salamatu Ari sun bayyana wa wakilinmu cewa kisan gillar da aka yi wa dan uwansu da keta inda suka nuna razanarsu dangane da lamarin. Daga nan sai suka roki ga jami’an tsaro su bi musu hakkinsu wajen kamowa da hukunta wadannan miyagun mutane.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Nasarawa, ASP Norman Usman da wakilinmu ya tuntube shi kan lamarin ya ce har zuwa lokacin rundunar ba ta samu labarin ba, amma za su gudanar da bincike a kan lamarin.
Aminiya ta gano cewa yawaitar kisan gillar da ake yi wa wadanda ba su ji ba ba su gani ba a garin Doma da kewayenta da ba a san masu yi ba, ya kasance abin fargaba da ke saka tsoro a zukatan al’ummar yankin.