Matsafa sun yanke mazakutar dan shekara 2 a Neja

Wasu da ake zargin matsafa ne sun gutsure mazakutar wani yaro domin hada layar bata a garin Pandogari da ke Karamar Hukumar Rafi a Jihar Neja. 

Matsafa sun yanke mazakutar dan shekara 2 a Neja

Jami’in hukumar tsaro na Sibil Difens (NSCDC) a jihar Neja

Wasu da ake zargin matsafa ne sun gutsure mazakutar wani yaro domin hada layar bata a garin Pandogari da ke Karamar Hukumar Rafi a Jihar Neja. 

Matsafan sun kuma sace wata budurwa suka yi mata fyade, kafin dubunsu ta cika.

Da yake gurfanar da wadanda ake zargin, Kwamandan Hukumar tsaro ta Sibil Defens (NSCDC) na Jihar Neja, Joachin Okafor, ya ce matasan da suka yi wannan aika-aikan sun amsa laifinsu.

Kwamanda Joachin Okafor ya ce matasan ne suka “yanke mazakutar yaron dan shekara biyu, kuma suka yi wa yarinyar ’yar shekara 13 fyade domin yin layar bata da kuma maganin bindiga.

“Sun sace budurwar ce da dan yaron a lokacin yana dan shekaru biyu, suka yanke masa mazakuta suka yanki marar yarinyar suka hada jinin da maniyyi da kuma mazakutar suka saka a wata kwalba suka kai wa bokansu,” in ji shi.

Yarinyar ta fallasa su ne bayan shekara biyu da faruwar lamarin inda ta kai kara hukumar sibil defens.

Mahaifin yaron ya ce, abokinsa ne ya sace yaron ya kai wa matsafan domin su kashe shi.

Jagoran matsafan ya amsa laifinsu a gaban jama’a ya kuma ce ba zai so a yi wa dansa abin da suka yi wa yaron ba.

“Sharrin shaidan ne ya sa muka biye wa Baba Sanda (bokan), amma muna roko a yi mana afuwa, ina da yaro guda daya, ba zan so ayi masa haka ba,” in ji shi.

Mahaifin yarinyar da aka yi wa fyaden ya ce yana rokon hukuma ta bi masa hakkin ’yarsa.

Hukumar Sibil Difens ta sha alwashin tabbatar da hukunta wadanda ake zargin.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos