Matsafa sun yi yunkuri kwakule ido da cire harshen wani yaro

Mutane garin Tudun Saibu da ke karamar Hukamar Soba a Jihar Kaduna sun ga abin al’ajabi da ban tausayi inda wasu da ake zaton matsafa ne suka yi yunkurin kwakule wa wani yaro ido da kuma yanke masa harshe.Mahaifin yaron mai suna Muhammad Muhammad ya shaida wa wakilinmu a garin Tudun Saibu cewa “A ranar […]

Matsafa sun yi yunkuri kwakule ido da cire harshen wani yaro
Matsafa sun yi yunkuri kwakule ido da cire harshen wani yaro

Mutane garin Tudun Saibu da ke karamar Hukamar Soba a Jihar Kaduna sun ga abin al’ajabi da ban tausayi inda wasu da ake zaton matsafa ne suka yi yunkurin kwakule wa wani yaro ido da kuma yanke masa harshe.
Mahaifin yaron mai suna Muhammad Muhammad ya shaida wa wakilinmu a garin Tudun Saibu cewa “A ranar Laraba na bar gida domin tafiya aiki, kuma mun rabu da matata cewa za ta tafi unguwa, inda na yi mata gargadi cewa in za ta tafi lallai ta tabbatar ta shaida wa Ummi ta kula da su Ahmad. To ashe bayan fitarmu masu wasa da kura sun zo unguwar sai wannan yaro Ahmad dan shekara uku ya bi masu wasa da kura, su kuma ’yan uwansa suna ta nema ba su gan shi ba, to ni da kanena Ahmad sai muka hau babur muka shiga nemansa muna cigiya sai wata makwabciyarmu ta ce mana ga wani yaro can ba wando ba riga kuma ana zaton an yanke masa kai har ma ya yi kashi sabo da wuya.  Koda muka isa wurin ina ganin rigarsa na ce Ahmad ne nan da nan za mu dauko shi sai Sarkin Tudun Saibu ya ce a’a a je a sanar da ’yan sanda aka je aka sanar da su suka zo da mota muka dauke shi cikin jini. DPO ya ce akwai kudi muka c babu ya ba da kudin mai Naira dubu uku ya ba mu Naira dubu biyar domin a kai shi asibiti nan da nan muka kai shi asibitin Wusasa inda aka fara kula da shi.
Ya kara da cewa “To muna can sai muka ji cewa an kama wanda ya aikata wannan mumman lamari ga wannan yaro har ma an ganshi da akwati da wukake biyar a cikin akwati kuma ana zaton ya dawo ne ya dauki yaron ya sa akwati Allah bai yi ba, sai mutane suka fara dukansa ’yan sanda suka dauke shi zuwa ofishinsu. Bayan mun dawo ’yan sanda suka gama bincikensu suka tura shi babban ofishinsu da ke Zariya.”
Malam Muhammad ya ce ba a yi nasarar kwakule ido ko yanke wani abu daga jikin dansa ba, sai dai an yi masa rauni a kokrin kwakule ido da cire harshensa.
A ofishin ’yan sanda na Tudun Saibu wani jami’i da bai so a ambaci sunansa ya ce wanda aka kama bisa zargin wannan aika-aika mutumin gangu ne kuma a buge yake da giya a lokacin ya taka sahun barawo, amma ba a kama kowa ba har zuwa yau sai dai suna nan suna gudanar da bikcike shi kuma wanda aka kama na farko an kai shi babban ofishinsu da ke Zariya domin su tantance gaskiyar lamarin kuma yanzu haka yaron yana samun sauki.