Matsahi ya kashe abokinsa saboda na’urar jin sauti a Kano

An gurfanar da wani matashi a Kano bisa zargin kashe abokinsa saboda na’urar jin sauti

Matsahi ya kashe abokinsa saboda na’urar jin sauti a Kano

Zama Kotu. (Hoto: Aminiya)

An gurfanar da wani matashi a kotu a Kano bisa zargin kashe abokinsa saboda naurar sauraren sauti ta Bluetooth.

Ana zargin matashin ya caka wa abokin nasa mai suna Abdulazeez Aliyu, wuka a ciki ne, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

Takardar karar ta bayyana cewa tun da farko wata sa-in-sa ce ta shiga tsakanin abokan biyu a kan abin saurare na wayar hannu (Bluetooth).

Sai dai wanda ake zargin ya musanta laifin da ake tuhumar sa da aikatawa na kisa wanda, ya saba da sashe na 221 a Kundin sharia na Pinal Kod.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Binta Ibrahim Galadanchi, ta Kotun Majistare Mai Lamba 19 da ke zamanta a Nomanslan ta bayar da umarnin tsare wanda ake zargin a gidan yari.

Daga nan ta dage sauraren shari’ar zuwa ranar 17 ga watan Janairu, 2023.

Lucky Aiyedatiwa ya lashe zaɓen Gwamnan Ondo

Ba na yi wa Tinubu hassada — Atiku

Kama matashiya kan sukar Gwamnan Sakkwato ya tayar da ƙura

Babban Limamin Minna Sheikh Isa Fari ya rasu