Matsalar albashi: Gwamnatin Tarayya da jihohi za su raba Naira biliyan 400

Buhari ya saki Naira biliyan 700 don samar da sauki Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da wasu shirye-shirye na ceto jihohin kasar nan da suka kasa biyan albashin ma’aikatansu, inda ya amince a raba Dala biliyan daya da miliyan 700, (kimanin Naira biliyan 413) daga cikin Dala biliyan biyu daga cinikin iskar gas.Shugaba Buhari […]

Matsalar albashi: Gwamnatin Tarayya da jihohi za su raba Naira biliyan 400
Matsalar albashi: Gwamnatin Tarayya da jihohi za su raba Naira biliyan 400

Buhari ya saki Naira biliyan 700 don samar da sauki

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da wasu shirye-shirye na ceto jihohin kasar nan da suka kasa biyan albashin ma’aikatansu, inda ya amince a raba Dala biliyan daya da miliyan 700, (kimanin Naira biliyan 413) daga cikin Dala biliyan biyu daga cinikin iskar gas.
Shugaba Buhari ya amince da haka ne a wani yunkurin da ake gani zai sa jihohin kasar su farfado daga cikin mummunan yanayin rashin kudi da suke ciki, inda a wasu jihohin aka shafe watanni babu albashi.
Shugaba ya kuma umarci Babban Bankin Najeriya ya bullo da wani shiri na musamman, wanda za a samar da kudin da za su kai Naira biliyan 300 domin bai wa jihohin a matsayin bashi mara tsauri.
Akanta Janar na Tarayya Ahmed Idris ne ya bayyana haka ga manema labarai na fadar Shugaban kasa bayan ganawa da Shugaban kasar a ranar Litinin.
Ahmed wanda aka nada a makon jiya, ya ce ya iske tsakanin Dala biliyan daya da miliyan 600 zuwa 700, inda ya ce za a raba wannan kudi a tsakanin fallayen gwamnati uku kamar yadda doka ta tanada. Sai dai bai bayyana yaushe za a raba kudin ba. Amma ya ce kwamitin zai rabon dukiyar kasa (FAAC) zai zauna a ranar ta Litinin don samun matsaya kan yadda rabon zai kasance kamar yadda Kwamitin Tattalin Arzikin kasa (NEC) ta yi umarni.
Kazalika, Shugaba Buhari ya amince da wani tsari na rage wa jihohi radadin biyan albashin, inda ya bullo da wasu hanyoyin uku nan a biyan basussukan albashi, ana jin za a fara aiki da wannan shiri a wannan mako kuma a hanzarta sake kudi cikin sauri.
Kakakin Shugaban kasa Garba Shehu ya tabbatar wa wakilinmu ta waya cewa lallai Shugaba kasar ya amince da wannan tsarin tallafi, inda za a sassauta wa jihohin basusukan da suka suka ciwo, su rika amfani da kudin a wasu fannoni na bunkasa rayuwar jama’arsu a maimakon biyan bashi gaba daya.
Za a samar da kudin ne ta hanyar sayar da iskar gas da tallafin Babban Bankin Najeriya da kuma na ofishin kula da basussuka (DMO). Kimanin jihohi 12 ne dai daga cikin jihohi 36 na kasar nan ne aka bayar da rahoton cewa ma’aikatansu na bin su bashin albashi na wata da watanni da kuma wasu kudaden alawus, da jimillarsu ta haura Naira biliyan 11.
Wata majiya ta gwamnati ta ce kudin da ma’aikata ke bi bashi a kasar nan sun kai Naira biliyan 250, domin akwai wasu ma’aikatan Gwamnatin Tarayya da su ma ba a biya su ba albashi ba wata da watanni.