‘Matsalar Arewa rashin hadin kan shugabanninta ne’

Wani dan Arewa mazaunin Benin a Jihar Edo Alhaji Jibrilla Abdullahi ya ce rashin hadin kan shugabannin Arewa ne babban abin da ya jefa yankin cikin matsaloli da koma baya, inda ya bukaci shugabannin su sake tunani da nuna halin dattaku su hada kai don nema wa yankin zaman lafiya da kawar da talauci da […]

‘Matsalar Arewa rashin hadin kan shugabanninta ne’
‘Matsalar Arewa rashin hadin kan shugabanninta ne’

Wani dan Arewa mazaunin Benin a Jihar Edo Alhaji Jibrilla Abdullahi ya ce rashin hadin kan shugabannin Arewa ne babban abin da ya jefa yankin cikin matsaloli da koma baya, inda ya bukaci shugabannin su sake tunani da nuna halin dattaku su hada kai don nema wa yankin zaman lafiya da kawar da talauci da al’ummar yankin suke ciki .

Alhaji Jibirilla ya bayyana haka ne a zantawarsa da Aminiya a garin Benin inda ya ce “Maganar gaskiya ita ce shugabanni ’yan siyasa na Arewa su dawo su hada kai in suka yi wannan to, lallai Arewa za ta samu ci gaba tare da zaman lafiya.”
Alhaji Jibril Abdullahi ya yi kira ga daukacin al’ummar Arewa cewa su tashi daga barcin da suke yi kuma su yi watsi da duk wani sakaci su yunkura don nema wa yankin Arewa ci gaba da zaman lafiya. “Ba zai yiwu shugabanni su sauke wannan nauyi su kadai ba tare da hadin kan jama’a ba, muddin ana son gaskiya,” inji shi.
Ya ce su mazauna Kudu abin da ke faruwa a Arewa yana damunsu ba kadan ba kasancewa babu zaman lafiya a wasu sassa na yankin har wasu suna yi musu gori da wannan.