Matsalar Ebola: Ko Ya Dace A Dakatar Da Gasar Cin Kofin kwallon kafa Na Afirka?

Ana ta kai kawo wajen ganin kasar da ta dace ta dauki gasar kwallon kafa ta cin kofin Afirika saboda ana tsoron kamuwa da cutar Ebola, wacce ta yi kamari a wasu kasashen Afrika. A yanzu dai an yanke cewa kasar Ekuetorial Guinea ce za ta dauki bakuncin gasar. Abin tambaya a nan shi ne, […]

Matsalar Ebola: Ko Ya Dace A Dakatar Da Gasar Cin Kofin kwallon kafa Na Afirka?
Matsalar Ebola: Ko Ya Dace A Dakatar Da Gasar Cin Kofin kwallon kafa Na Afirka?

Ana ta kai kawo wajen ganin kasar da ta dace ta dauki gasar kwallon kafa ta cin kofin Afirika saboda ana tsoron kamuwa da cutar Ebola, wacce ta yi kamari a wasu kasashen Afrika. A yanzu dai an yanke cewa kasar Ekuetorial Guinea ce za ta dauki bakuncin gasar. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a dakatar da gasar ta bana saboda tsoron cutar ta Ebola ko bai dace ba? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana na ra’ayoyin mutane daban-daban:

Ya kamata a dakatar da gasar  – Mu’awiya Abubakar

A.A. Masagala, a Benin

Alhaji Mu’awiya Abubakar: “A gaskiya ni a ra’ayina, ina ganin ya kamata a dakatar da wannan wasan har sai an tabbatar da babu batun Ebola a nahiyar Afirika gaba daya. Saboda haka a dage batun wasan har zuwa wani lokaci nan gaba, domin kare lafiyar jama’a daga wannan cutar Ebola mai yaduwa. Kuma ko da za a yi wannan wasan, ya zama wajibi ga Hukumar kwallo kafa Ta Duniya (FIFA) ta fito da wata hanyar bincike ta tantancewa ga duk mai shiga filin wasan da ’yan wasan da ’yan kallo, domin idan ba hakan aka yi ba to lallai ba mamaki mutane da dama za su iya kamuwa da wannan cutar Ebola kai tsaye.

Dakatar da gasar shi ya fi – Musa Abubakar

A.A. Masagala, a Benin

Malam Musa Abubakar: “A ganina, batun a yi wannan wasan bai dace ba sam sam. Dalilina shi ne ganin halin da al’umma na wasu kasashen Afirkan suke fama a ciki na annobar cutar Ebola. Don haka a yanzu ba batun wasa ko cin kofi ne yake a gaban kowane dan Afirika mai hankali ba, a’a yaya za su yi su samu hanyar kawar da cutar Ebola ta fi damun su. Don haka cewa Hukumar kwallon kafa Ta Afirika (CAF) ta ce za ta gudanar da wani abu mai suna wasan cin kofi, hakan sam bai dace ba. Idan har ta yi hakan, ya nuna a fili ita ba ta damu da wannan annobar da al’ummar nahiyar take fama da ita ba.

Gasar za ta iya yada cutar – Jafaru Madobi

Mohammad Yaba, a Kaduna

Malam Jafaru Na Sa’a da Sa’a Madobi: “Ba na goyon bayan a yi wasan saboda idan aka yi za a sake kawo mana cutar Ebola a Najeriya. Don haka ni ba na goyan bayan a yi gasar. Babu kuma wani mataki da za su dauka domin hana yaduwar cutar a tsakanin jama’a, domin dama can kawo cutar aka yi Afirika sannan aka yada ta. Ka ga ke nan idan aka yi wasan kwallon akwai yiwuwar ’yan Najeriya da za su je can kasar da za a yi wasan su iya sake debo cutar zuwa kasar nan.”

Bai kamata a dakatar da gasar ba – Haruna Suleiman

Mohammad Yaba, a Kaduna

Haruna Suleiman Jami’ar Ahmadu Bello Zariya: “Bai dace a soke gasar kwallon ba saboda cutar Ebola. Ai ko’ina akwai cuta saboda haka a je kawai a buga wasa saboda kwallo tana hada kan mutanen duniya ne baki daya. Abin da kawai ya dace su yi shi ne, a dau matakin kare al’umma daga cutar ta Ebola, ta hanyar gwada duk wanda zai shiga gasar ko kallo amma bai kamata a hana wasan ba.”

Bai kamata a dakatar da gasar ba – Mumammad Bashir

Muhammad danladi Ibrahim, a Minna

Malam Muhammad Bashir Abacha: “A gaskiya bai dace a dakatar da gasar ba, domin kuwa babu inda babu cuta. Bai kamata a ce nahiyar da ta shahara game da harkar kwallon kafa a ce ta ki daukar nauyin gasar da ke taimakawa wurin hada kan jama’a don wata cutar da ta bulla a wata kasa ba. Maimakon janye daukar nauyin gasar, kamata ya yi a ce ta dauki matakan da suka kamata tun daga filin saukar jiragen sama don duba kowane dan wasa da jami’ansu domin tabbatar da ko suna dauke da cutar ko babu. Abin da kasar da za ta dauki nauyin gasar ta yi shi ne, ta tabbatar da an tantance duk wanda zai shiga cikin kasar daga farko zuwa karshe don tana da kayan aikin da suka kamata.”

Kada a soke gasar – Kwamred Hamisu

Muhammad danladi Ibrahim, a Minna

Kwamred Hamisu Musa Jankaro: “Bai kamata a ce an kai ruwa rana tsakanin kasar Moroko da Hukumar Kula da Harkokin kwallon kafar Nahiyar Afrika ba saboda lamarin cutar ebola. Da ma can kasar ba ta shirya daukar nauyin gudanar da gasar ba, shi ya sa ta fake da guzuma ta harbi karsana. Ita fa cuta duk inda mutum yake idan Allah Ya kaddara zai harbu da ita, babu tsimi babu dabara sai ya kasance. Maimakon janyewa baki daya kamata ya yi a ce ta dauki matakan da suka kamata na hana yaduwar cutar, yadda Najeriya da sauran kasashen duniya suke yi. Gaskiya kasar Guinea da aka ba ta alhakin gudanar da gasar za ta iya, shi ya sa aka ba ta. Tana da filayen wasa masu kyau shi ya sa ba a yi shakkar ba ta izinin gudanarwa ba.”