Matsalar fetur na jawo wa talaka matsala
Duba da irin ganin yadda tun dawowar mulki ga farar hula har ya zuwa wannan lokaci, ana cikin mawuyacin hali na rashin isasshen man fetur a duk lokacin da aka ce bukukuwan Kirsimeti ko na Sallah sun zo, to a daidai lokacin duk wani talaka mai mu’amala da wani karfen hawa, ya shiga cikin wani […]
Duba da irin ganin yadda tun dawowar mulki ga farar hula har ya zuwa wannan lokaci, ana cikin mawuyacin hali na rashin isasshen man fetur a duk lokacin da aka ce bukukuwan Kirsimeti ko na Sallah sun zo, to a daidai lokacin duk wani talaka mai mu’amala da wani karfen hawa, ya shiga cikin wani hali na tazauniya a kan matsalar mai, wanda duk wani dan kasa tambayar da zai yi ita ce, shin man ne babu? Ko dai babu masu dakon man ne zuwa lunguna da sako-sako, inda ake son man ya kai? Shin ko dai kuwa ana voyen man ne domin talaka ya shiga cikin halin ni a su?
Domin kuwa rashin man ya saka wasu da yawa aje ababen hawansu, saboda matsanancin mai, wanda yake addabar talakawa a daidai wannan lokaci, Yanzu haka a cikin wasu gidajen mai ana sayar da man a ƙalla 175 duk lita daya, sannan ga cincirindon dinbin al’ummar da za ka ci karo da su.
Shakka babu a Najeriya duk lokacin da kasa ta shiga cikin wani hali, a kan talaka komai yake karewa domin shi ne wanda ba shi da wani galihu, a bisa ga wannan ne ya sa a kowane lokaci talaka cikin kuka yake, kuma har yana sa wa zuciyarsa shin anya kuwa gwamnati ta san da zamansa, na cikakken dan kasa kuwa? Wannan ne yake saka wasu talakawa cikin bakin ciki da takaici da nadama, inda suke tuna cewa su fa suka yi zavi. Kuma suka kasa, suka raka kuma suka jira, amma yanzu ga shi nan an maida su ba kowa ba,
A bisa wannan ne muke kira da babbar murya ga karamin ministan mai na kasa, da jagororin da hakkin dakon man ya rataya a wuyansu da su dubi yiwuwar kawo karshen wannan matsalar domin talakawa su samu sa’ida, hadi da dawowar hada-hada da zirga-zirga a cikin al’umma.
A karshe ina addu’ar samun yalwataccen arziki da zaman lafiya a Najeriya gaba daya. Bissalam
Mai Apple ya rubuto makalarsa daga Gusau, dan kungiyar Muryar Talaka ta kasa reshen Jihar Zamfara (08133376020/08086679022 nura Muhammad Gusau <[email protected]>