Matsalar Iran ta fi ta ISIS illa – Netanyahu
Firayi Ministan Isra’ila Mista Benjamin Netanyahu, ya yi gargadi ga kasashen duniya cewa, barin Iran ta mallaki makamin nukiliya abu ne da ya fi kungiyar ISIS muni fiye da sau dubu. Mista Benjamin Netanyahu ya ce kungiyar ISIS barazana ce, amma ya danganta Iran a matsayin kasar ’yan ta’adda.Firayi Minista Netanyahu ya ce matukar Iran […]
Firayi Ministan Isra’ila Mista Benjamin Netanyahu, ya yi gargadi ga kasashen duniya cewa, barin Iran ta mallaki makamin nukiliya abu ne da ya fi kungiyar ISIS muni fiye da sau dubu.
Mista Benjamin Netanyahu ya ce kungiyar ISIS barazana ce, amma ya danganta Iran a matsayin kasar ’yan ta’adda.
Firayi Minista Netanyahu ya ce matukar Iran ta mallaki makamin nukiliya za ta fi kungiyar ISIS da ke da’awar jihadi a kasashen Syriya da Iraki mugunta fiye da sau dubu.
Kalaman Shugaban na daular Yahudawa na zuwa ne a yayin da kwararru daga bangaren Iran da manyan kasashen duniya ke shirin ganawa a bienna kafin cikar wa’adin cimma yarjejeniyar nukiliyar a ranar 30 ga watan Yuni.
Mista Netanyahu ya dade yana adawa da sasantawar da kasashen Amurka da Birtaniya da Faransa da Rasha da Jamus ke yi da Iran don cimma yarjejeniya da ita a kan yadda za ta dakatar da shirintana nukiliya, wadda Iran din ta bayyana da na zaman lafiya ne domin samar da makamashi.