Matsalar kisa da sace ’yan acaba ta addabi Keffi
Matsalar yawan kashe masu sana’ar acaba tare da cire sassan jikinsu a garin Keffi ta Jihar Nassarawa na kara ta’azzara, a yayin da wasu masu sana’ar kuma ake yin awon gaba da su da ransu, ba tare da an dauki baburansu ba. Wakilinmu wanda ya ziyarci garin a ranar Litinin da ta gabata, ya samu […]
Matsalar yawan kashe masu sana’ar acaba tare da cire sassan jikinsu a garin Keffi ta Jihar Nassarawa na kara ta’azzara, a yayin da wasu masu sana’ar kuma ake yin awon gaba da su da ransu, ba tare da an dauki baburansu ba. Wakilinmu wanda ya ziyarci garin a ranar Litinin da ta gabata, ya samu labarin cewa sakamakon matsalar, karamar Hukumar Keffi ta ayyana dokar hana acaba daga faduwar rana zuwa wayewar gari.
Matsalar dai kamar yadda majiyoyii da suka zanta da Aminiya suka bayyana, ta faro ne kimanin wata shida, sannan ta kara muni a watan Disamba, inda a ranar Juma’ar makon jiya aka tsinci gawarwakin ’yan acaba hudu a unguwar GRA da ke Keffi, wadanda uku daga cikinsu an cire wasu sassan jikinsu, ba tare da an wuce da baburansu ba. An kuma samu wasu gawarwaki biyu a wani yanki na garin kwana biyu bayan haka.
A bangaren sace masu sana’ar kuwa, majiyar Aminiya ta ce na baya-bayan nan shi ne wanda ya rutsa da wasu masu sana’ar su biyu wadanda aka yi awon gaba da su a wani yanki na garin, a daidai lokacin da suke wanke baburansu tare da wani da ke sayar da rake, kamar yadda wadanda suka shaida al’amarin suka bayyana, daga baya.
Sakataren masu sana’ar acaba na garin Keffi Kwamared Idris A. Sule, a yayin zantawarsa da wakilinmnu ya ce, wadanda suka sace mutum uku daga cikinsu sun tilasta musu shiga motarsu kirar Jeep ne, bayan sun nuna masu bindiga.
Game da mutum hudu da aka same su a mace kuwa, sakataren ya ce biyu daga cikinsu ’yan asalin jihar ne daga karamar Hukumar Kokana, a yayin da saura biyun kuwa daya dan Jihar Katsina ne daya kuwa dan Jihar Bauchi.
Wani dan acaba da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce mambobinsu suna kaurace wa aiki a wasu wurare na garin bayan an gano gawarwakin masu sana’ar a wajen, ya ce yankunan su ne: karamin filin saukar jirgin sama da bayan filin bal, sai kuma hanyar Jama’a, duk a garin Kefffi.
A sakatariyar karamar, shugaban karamar hukumar Malam Muhammad Yahaya Dikko, ya shaida wa wakilinmu cewa, bayan aukuwar lamarin, ya bukaci zama na musamman da shugabannin sassan tsaro da ke yankin inda suka yanke shawarar dakatar da acaba daga karfe 7:00 na yamma zuwa 6:00 na safe. Ya ce bayan sun bukaci kundin sunayen masu sana’ar daga shugabanninsu, sun nanata dokar tilasta sayen rigar jaket ga masu sana’ar. Babban Jami’in ’Yan sanda (DPO) na Keffi wanda ya tabbatar da faruwan lamarin, ya ki yin karin haske a kai, inda ya ce Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Nassarawa da ke Lafiya ne ke da hurumin yin bayani a kan al’amarin.