Matsalar Onnoghen: Lauyoyi sun juya wa umarnin kungiyarsu baya

Rahotanni daga jihohi daban-daban sun nuna yadda wadansu daga cikin lauyoyi a Najeriya suka kaurace wa umarnin kungiyarsu ta kasa ta bayar dangane da yajin aiki wuni biyu da ta nemi su yi, domin nuna rashin amincewa da matakin da Gwamnatin Tarayya ta dauka na dakatar da Babban Jojin Najeriya, Mai shari’a Walter Onnoghen. A […]

Matsalar Onnoghen: Lauyoyi sun juya wa umarnin kungiyarsu baya
Matsalar Onnoghen: Lauyoyi sun juya wa umarnin kungiyarsu baya

Rahotanni daga jihohi daban-daban sun nuna yadda wadansu daga cikin lauyoyi a Najeriya suka kaurace wa umarnin kungiyarsu ta kasa ta bayar dangane da yajin aiki wuni biyu da ta nemi su yi, domin nuna rashin amincewa da matakin da Gwamnatin Tarayya ta dauka na dakatar da Babban Jojin Najeriya, Mai shari’a Walter Onnoghen.

A Ibadan fadar Jihar Oyo, lauyoyi sun juya wa yajin aikin baya, inda aka gan su da yawa sun cika kotuna, inda harkokin shari’a suka rika gudana a ranar Talata da ta gabata kamar kullum. Masu shari’a a Kotu ta 17 da ke Gundumar Iyaganku sun fito aiki amma daga bisani sai ga jami’an Kungiyar Luyoyi ta Najeriya reshen Jihar Oyo sun halarci kotun, inda suka sanar da masu shari’ar da lauyoyin da ke harabar kotun cewa kungiyarsu tana yajin aiki na wuni biyu.

A Jihar Benuwai kuwa, rahotannin sun ce wadansu lauyoyin sun yi mubayi’a ga umarnin kungiyar, yayin da wadansu suka bijire. A garuruwan Otukpo da Makurdi, lauyoyi sun kaurace wa kotuna, duk da cewa an ga al’amura na gudana a harabobin kotunan. Shugaban kungiyar na Jihar Benuwai, Caleb Ishember ya bayyana wa manema labarai cewa su dai a bangarensu, an samu mubayi’a ga umarnin uwar kungiya da kashi 80 cikin 100, yayin da kashi 20 ne kadai suka bijire.

A Jihar Jigawa ma an samu rahoton cewa lauyoyi sun yi biris da umarnin uwar kungiyar, inda suka fita aiki a kotuna daban-daban domin gudanar da ayyukansu. Shugaban Kungiyar Lauyoyi reshen Jihar Jigawa, Bashir Usman ya ce: “Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya reshen Jihar Jigawa ba za ta shiga wani yajin aiki ba kuma ba za ta kaurace wa halartar kotuna ba. Kungiyarmu tana nuna damuwarta dangane da abin da ya faru ga bangaren shari’a a wannan lokaci na dakatar da Babban Jojin Najeriya. Wannan lokaci ne na kalubale ga al’amuran shari’a Najeriya,” inji shi.

A jihohin Kogi da Adamawa da Gombe ma, ba a samu cikakkiyar biyayya ga umarnin uwar kungiyar lauyoyin ba, domin rahotannin sun tabbatar da cewa wadansu lauyoyin sun fita aiki kamar yadda aka saba, wadansu kuma ba su fita ba.

Sojoji sun kashe kwamandan ’yan bindiga da tarwatsa 300

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta