Matsalar Rashin Bayyana Soyayya
Assalamu Alaikum Makarantanmu, barkanmu da sake saduwa a cikin wannan fili, da fatan Allah SWT Ya amfanar da mu dukkan bayyanan da za su zo cikinsa, amin. Ga karashen bayani kan matsala ta farko cikin matsalolin auratayyar Bahaushe daga makon jiya, da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma […]
Assalamu Alaikum Makarantanmu, barkanmu da sake saduwa a cikin wannan fili, da fatan Allah SWT Ya amfanar da mu dukkan bayyanan da za su zo cikinsa, amin. Ga karashen bayani kan matsala ta farko cikin matsalolin auratayyar Bahaushe daga makon jiya, da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
Abubuwan Hana Bayyanar Soyayya… Ci gaba
5. Rashin Kayan Cajin kauna:
Kayan cajin kauna su ne abubuwan da ke dumama so da kauna da zafafa soyayya tsakanin ma’aurata; sun kunshi yawan runguma da sumbatar juna, musamman lokacin gaisawa, lokacin yi tarbar juna da lokacin yin ban kwana. Sai kallo da hararar masu bayyanar da so da kauna; murmushin nuna kauna da sauransu. Yanayin al’adar Bahaushe ta sa kwata-kwata babu abubuwan dumama soyayya da bayyana kulawa wajen wanzar da dangantakar auratayya. Wasu ma’auratan ko a wajen ibadar aurensu ba su yin wadannan abubuwan caza soyayyar; don haka akwai da yawan ma’auratan da har su gama rayauwarsu ba su taba sumbatar juna ba. Sannan ba su rungumar juna don nuna kauna kawai ba runguma ta sha’awa ba. Ya kamata Malam Bahaushe ya aje al’adarsa ta rashin wadannan kayan cajin kauna cikin auratayya; ya aro daga Larabawa da Turawa sannan ya al’adantar da ita cikin rayuwar aurensa. Ko kuma dabbakar da ita a matsayinta na kyakkyawar Sunnar Annabi SAW kamar yadda aka dabbaka sunnar yin musabaha yayin gaisawa da juna; domin wadannan abubuwa suna da matukar alfanu wajen gina aure da inganta shi; sannan ga shi kasancewarsu ibada ne domin suna daga cikin sunnar Manzon Allah SAW.
6. Rashin Kula
Wasu ma’auratan kuwa suna zaune zaman aure ne, amma ba su ma san cewa su masoya ba ne, balle har su rika kokarin bayyanar da wannan soyayya ga juna, ko su rika kokarin kula da soyayyar nan ta yadda za ta inganta rayuwar aurensu; aure kawai suke, wanda ba so da kauna ko tausayin juna a cikinsa; wannan za ka tarar ba su more zaki da dadi da ke cikin rayuwar auratayya ba.
7. Rashin Dacewar Ma’aurata
Shi ma wannan babbar matsala ce da ke hana ma’aurata bayyanar da soyayyarsu ga juna, domin kuwa Hausawa na cewa sai hali ya zo daya sannan ake abota; to haka ma wajen rayuwar aure, in aka sami bambanci mai girman gaske tsakanin ma’aurata, musamman ta fannin halayya, ra’ayi da yanayin zamantakewa, wannan zai haifar da yawan gardama da yawan husuma cikin rayuwar auren, a haka sai ya kasance ba mai iya bayyanar da soyayya ga dan uwansa saboda wannan bambancin da ke tsakaninsu.
8. Cushewar Hanyar Sadarwa
Akwai ma’auratan da, zuciyarsu fal take cike da so da kaunar juna, amma rashin budaddiyar hanyar sadarwa tsakaninsu ya sa ba su iya bayyanar da so da kaunarsu ga juna, suna dai zaune zaman taimake ni in taimake ka, amma ba zakin so da kauna cikin autayyarsu.
9. Rashin Haduwar Kan Ma’aurata:
Idan ya kasance kan ma’aurata ba a hade yake ba, ba su cure sun zama daya ba ta kowanne fannin rayuwar ba, kowannensu ya ware yana harkokinsa daban da dan uwansa; to irin haka yana tsananin gurgunta soyayyar da ke tsakanin ma’aurata; sannan ya hana su bayyana so da kaunarsu ga juna. Domin babban makasudin aure shi ne hada abubuwa biyu su zama abu guda; mutum biyu daban-daban din juna ta hanyar halitta da dabi’a su zama aure daya; ma’auratan da ke da irin wannan hali sun karya babban tubalin da ya gina aure a tsakaninsu.
10. Ginuwar Iyali
karuwa da cikar iyali na hana ma’aurata bayyanar da soyayyarsu ga juna; sai ya kasance ma’aurata sun yi musayar so da kauna da kulawar da ke tsakaninsu zuwa ga ‘ya’yansu; kowannensu ta ‘ya’ya yake amma ba ya ta masoyinsa abokin aurensa; wannan babban kuskure ne da ma’aurata ke yi, ya kamata a ce ginuwar iyali ta kara fito wa ma’aurata sababbin hanyoyin nuna so da kauna ga junansu ba ta dakile su ba.
Ma’aurata su sani cewa, aure wani abu mai gudana; ba za a so duk wani abun da zai kawo cikas ga gudanar rayuwar aure ba; so da kauna sun kasance su ne karfin gudanar koramar auratayya; don haka duk ma’auratan da ke son su albarkatu da koramar aurensu, lallai su yi kokarin gyaran magudanar soyayyarsu; su yi kokarin taba duk wata komada da ke kawo cikas ga so da kaunar da ke tsakaninsu; su dage wajen bayyanar da soyayyarsu ga juna; don karawa da tabbatar farin ciki, aminci da inganci cikin rayuwar aurensu.
Zan dakata a nan, sai sati na gaba insha Allah, bayani na zuwa ga hanyoyin bayyanar da soyayya tsakanin ma’aurata; da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.