Matsalar rashin bayyanar da soyayya a tsakanin ma’aurata (2)
Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh; barkanmu da sake haduwa a wannan fili da fatar Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani kan matsalar rashin bayyanar da soyayya a tsakanin ma’aurata. Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma Ya amfanar […]
Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh; barkanmu da sake haduwa a wannan fili da fatar Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani kan matsalar rashin bayyanar da soyayya a tsakanin ma’aurata. Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma Ya amfanar da su, amin.
- Rashin kula
Wadansu ma’auratan kuwa suna zaune zaman aure ne, amma ba su ma san cewa su masoya ne ba, balle har su rika kokarin bayyanar da wannan soyayya ga juna, ko su rika kokarin kula da soyayyar nan ta yadda za ta inganta rayuwar aurensu; aure kawai suke, wanda ba so da kauna ko tausayin juna a cikinsa; wannan za ka tarar ba su more zaki da dadi da ke cikin rayuwar aure ba.
- Rashin dacewar ma’aurata
Shi ma wannan babbar matsala ce da ke hana ma’aurata bayyanar da soyayyarsu ga juna. Domin kuwa Hausawa na cewa sai hali ya zo daya sannan ake abota; to haka ma wajen rayuwar aure, in aka samu bambanci mai girman gaske tsakanin ma’aurata, musamman ta fannin hali, ra’ayi da yanayin zamantakewa, wannan zai haifar da yawan gardandami da yawan husuma cikin rayuwar auren, a haka sai ya kasance ba mai iya bayyanar da soyayya ga dan uwansa saboda wannan bambanci da ke tsakaninsu.
- Cushewar hanyar sadarwa
Akwai ma’auratan da zuciyarsu fal take cike da so da kaunar juna, amma rashin budaddiyar hanyar sadarwa tsakaninsu ta sa ba su iya bayyanar da so da kaunarsu ga juna. Suna dai zaune zaman ‘taimakan ni in taimake ka,’ amma ba zakin so da kauna cikin autayyarsu.
- Rashin haduwar kan ma’aurata:
In ya kasance kan ma’aurata ba a hade yake ba, ba su cure sun zama daya ba ta kowanne fannin rayuwarsu, kowannensu ya ware yana harkokinsa daban da dan uwansa; to irin haka yana tsananin gurgunta soyayyar da ke tsakanin ma’aurata; sannan ya hana su bayyana so da kaunarsu ga juna. Domin babban makasudin aure shi ne hada abubuwa biyu su zama abu guda; mutum biyu daban-daban ta hanyar halitta da dabi’a su zama aure daya; ma’auratan da ke da irin wannan hali sun karya babban tubalin da ya gina aure a tsakaninsu.
- Ginuwar iyali:
Karuwa da cikar iyali na hana ma’aurata bayyanar da soyayyarsu ga juna; sai ya kasance ma’aurata sun musayar da so, kauna da kulawar da ke tsakaninsu zuwa ga ’ya’yansu; kowannensu ta ’ya’ya yake amma ba ya ta masoyinsa abokin aurensa; wannan babban kuskure ne da ma’aurata ke yi. Ya kamata a ce ginuwar iyali ta kara fito wa ma’aurata sababbin hanyoyin nuna so da kauna ga junansu ba ta dakile su ba.
Ma’aurata su sani cewa, aure wani abu ne mai gudana; ba za a so duk wani abin da zai kawo cikas ga gudanar rayuwar aure ba; so da kauna sun kasance su ne karfin gudanar koramar auratayya; don haka duk ma’auratan da ke son su albarkatu da koramar aurensu, lallai su yi kokarin gyaran magudanar soyayyarsu; su yi kokarin tada duk wata komada da ke kawo cikas ga so da kaunar da ke tsakaninsu; su dage su rika bayyanar da soyayyarsu ga juna; don karawa da tabbatar farin ciki, aminci da inganci cikin rayuwar aurensu.
Zan dakata a nan, sai mako na gaba insha Allah, da fatar Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.